KARYAR WUSULI
Zancen wusuli ba da tababa ba Mun yarda karya ce ta mai yin zama Ba wani tajalli ba fana'i sannan Balle barin taklif ibadun kenan Wallahi hanyar nan ta shaidani ce Ku biyo tafarki in kuna son dace Duk wanda yai shirka ga Allah Jalla Sai ya zamo iccen jahannama tallah Inyasi ko ku sani fa ba Allah ba Kuma bai fi Manzo gun yawan daraja ba Na san ka na zagi idan na tuna ma To shi kwa zagi kari na gaya ma Allahu dai ne bai abokin tare Kuma bai kini duk na fada kun shude In kun ki ji ku sani ba kwa ki gani ba Ranar shiga Saqara da Lazza duba