Posts

Showing posts from September, 2021

DABI'UN GIRMA

Gatanan ku zauna ku jita Wakar yabo ce na yi ta Kan jagaban duk halitta Halinsa ne zan rubuta Duk da sanin da nai ya ƙaranta Ya shugaban duk halittu Na Khadija Abba ga Bintu In har ka na son mu jitu To ka fito ka so Ɗa na Shitu Kyan akhlaku an bashi tuta Nai jinjina har da godo Gun Rabbana nawa dodo Dunyarga Shi zai yi gado Sannan matattu ya tado Ranar nuna Gwarzon halitta Kai sallama har salati Gun Hamidan mai kanati Masanin cikar naka Zati Har ahlihi har banati A ciki har ka sanya da Binta Begenka zai sa na zautu Ya zanyi ne in kusantu Ga ba karatu rubutu A fagen yabon banda hutu Koda zan jiki yajjigata Na tashi kuka na ke yi Ihu na ke harda wiyi Na rassa ya za na ma yi Kaunarka Mahmudu Mahyi Kar fa ta zam silar hallakata Ya mai dabi'u na girma Aiko ka yai don ka cimma Wannan batu ya yi shi ma Halayensa Qur'an ka kama Ko can ba shi karya da mita Ko Jalla ma yai yabonsa Kan ɗaukakar lammarinsa Da makarimun yai batunsa Farkon Noon idan dai ...

Badaɗina

Badaɗina Ma'aiki Sidi Ahmad Uban Abdullah Manzona Muhammad Da sonka na kwan da shi ne za na tashi A kullum zan yabon nan babu fashi Ina koyi da Hassan shugabanmu A baitocin da yaiwa Annabinmu: "Kamar kyawunka babu idon da yagga A kyawu ka wuce waccan da wagga Fa babu macen da tahhaifo shigenka Kamar dai ma nace kai kayyi kanka Da an haifoka tas sam babu aibu Kamar haka nan kaso Manzo Habibu" Na kan shiga ɗimuwa in an faɗeka Da shauƙi wanda nasan baida tamka Idanu na cika tambam da ƙwalla Akan begenka ya Manzo na Allah Kusanci ne nake so nan gabanka A ba sallah gareni bare fa zakka Ina ɗan sujjada sai ɗan salati A sani maƙotaka don Rabbu Zati A lamuncen na zam wani hadiminka Da in ka cire su takalma na ɗauka Ina tafiya a bayan Sidi namu Idan ya sha ya ban ni ne da  kamu Idan ya cire sahu nasa ni na taka Kamar Bila fa bawan nan na Makka Ina roƙonka Allah don isarka Acan Firdausi kaini ga Annabinka Gama ni duniyar nan ban da buri Da yawwuce lahi...

Maraba da Masoya Waƙoƙin Yabon Manzo ASW

 Assalamu alaikum. Barkanku da shigowa wannan shafi mai albarka na yabon Fiyayyen Halittun Allah ASW. Za mu dinga kawo muku rubutattun ƙasidun yabon Manzo waɗanda aka tsara a tsanaƙe don kaucewa salon yabon da Annabi sam baya farin ciki da su da mu ke ji su na yawo a gari. Idan zaka yabi Annabi ASW amma kuma ka taɓa martabar wani Annabin ko kuma ka faɗi abinda sam bai dace ba a haƙƙim shi Shugaba ASW, to sam Annabi ba zai karɓi wannan a matsayin yabo ba sai dai zambo. Allah mu ƙe roƙon da ya yi mana jagora kada mu zarme ko kuma mu tauye ɗaya daga martabobin Manzo ASW. Sannan mun ɗau ɗamarar kare Manzo da ga dukkan wani zambo ko xane ko eani furuci da wasu maƙiya Musulunci ke yi a duk sanda su ka aikata hakan. Wannan alƙawari ne mu ka ɗauka sai dai fatan Allah ya ba mu damar saukewa lafiya. Mu na ƙara yi muku maraba lale da fatan za ku dinga yin sharhi a wajen da aka ware domin yin sharhi domin mu ƙara samun ƙwarin gwuiwar wallafa wasu sabbin ƙasidu yabo, tarihi,, ko bada kariya ga ...