Posts

Showing posts from December, 2022

BAKI YA YANKA WUYA

 YA YANKA WUYA Na fito kare Ma'aiki Mustaphan mu na Ummu-Hani Dukiya har rayuwata Za ni ba Ɗan Addanani Babu tsoro babu shakka Babu mai iya kakkaɓe ni Yau da kaka anka ƙare Duk da an fara da rani Yau hukunci ya yi kyawu Tunda an yanke bisani Audu ya yi ɓatan ɓatantan Babu tarko ba mayani Babu sauran ƴan tastine Tunda an rushe ɗayani Yanzu kogon ma kufai ne Babu shehin ƴan zamani Tauna tsakuwa don aya ne Na ji zancen Dakta Sani Isgili an kaiwa Nuru Mujtaba Kakan Husaini Rabbana ba zai bari ba Duba Hijri cikin Ƙurani "Mun isar maka isgilin su" Kunji Jalla ya na bayani Rabbu na kishin AbinSa Zai yi damƙar ne da tsanani Jinjina Ɗan Sarki Yola Malami kuma mai sukuni Ga hukunci ga sarauta Ga tilawar Al-ƙurani Maluman mu gaba ɗayan su Sun rawa ta gani da nuni Rabbana ya biya ku sannan Yai hanin duk ma su muni Zai saka a cikin biɗar ku Sanda anka aje ma'auni Sai salati har salami Kan sa jikan Addanani Alihi da dukan sahabbai Tabi'ai har Al-Bunani Ni Na'Annabi ne Muham...