Raina Fansar Ka
Ina ƙaunar Miji gun Nana Hafsa Iyayena da kaina gun ka fansa A sunan Rabbu Ƙhaliƙu ne na kan sa Idan zan fara komai don isar Sa Salat da salami ninninka akan sa Da rahma har da albarka akan sa Da mataye ka sa ahlin gidansa Sahabbai har da masu biyar sahun sa A bayan nan a yau zan nuna son sa A waƙen nan idan na bada amsa Ga mai neman dalilin nuna son sa Da arna masu batanci akansa Da fatan za su gane ina na dosa Gama sam ba su gane kala ta sonsa Muna ƙaunar sa ne ƙaunar da ke sa Mu bar komai idan shi za ya nisa Abu Sufyanu in na tuno batun sa Da ɗai bai san ba wanda ka so kamar sa A faɗin duniyar ga iya saninsa Mutum bai so waninsa ba sam kamar sa Sahabi ne ana cisgar jikinsa Ya ce bai son ƙaya fa ta je wajen sa Mu kan iya bada komai mu a kan sa Iyaye duk da dangi kansa fansa Riƙe al'ana ya Umari hadisa A son sa ku sa dukan komai ƙasansa Ku so shi ku bi shi ba mu da ɗai kamar sa Mu kare shi da alayen gidan sa