MAWADDAH
In kana jin fushi da anbaci Zahra Ko mijinta da Ƴan Tagwayen Yara Tofa malam ka je ka sauya dabara Don kwa tsatsa a zuciya ka tara Ya kamata mu saura duk kan tsari Don ƙiyayyar da kai da mai tattaki Kar ta sanya ka yin fushi da Ma'aiki Bai buƙatar kuɗin ku ko alkaki Sai mawaddah ga Ƴan Gida mai Tsarki Suratush-Shura je ka sumnin fari In watan haihuwarsa ma ya kama Babu kai ba faɗa da tada husuma Ƙungiyar ka daban da ta su kwa suma Za su ce baka son Uba gun Umma Shi fa Manzon mu ne Bashiri-Naziri To batu ne ake na ƙaunar Sidi Bugi ƙaimi ka sake tamke sirdi Tafiyar nan shigo ciki ba ƙaidi Bisa tsari kuje wajen Maulidi Inda hali ku shafa ma bandiri