Posts

Showing posts from January, 2022

KANWAR LASA

KANWAR LASA Fa Walidan Manzon mu gagara gasa Ina yabon kanwar da ta wuce lasa Bismillah Allah ni na ke farawa Sarkin da shi ne dai na ke bautawa Baya azaba tun gaban aikawa Zan yo yabon Abdullah harma Giwa Fa Walidan Manzon mu Angon Hafsa Cecekucen ne ya ki yai karewa Wai duk akan Abbansa har Yar Baiwa Fa Amina  yar Wahbi kin wuce kowa A duk matakai kunga  sun tserewa Mai son ku shi ne yau na ke rarrasa Maganganu ba kan gado mun ji su A bayyane tun da ana  boye su Akan makomar wai Iyayen Shamsu Wannan da shi ne yazzamo dawisu Ga duk ma'aika kunji dan Abbasa Yau na gaji shi ne na ke yin raddi Ga masu zance ba bu kai ba gindi Su na ta sukuwa sun hawa ba sirdi Ana ta zance kan Iyayen Hadi Wannan abin ya sa jini ya tafasa Ka na da riba in ya zamto ka ce Wannan karatun nan kamar ka zauce Kana fada harma kana wani huce A ranka gaba ko kiyayya dai ce? Ga Mujtaba Manzon mu raina fansa Wannan ya sa ma Audu yai tawaye Ya ce hadisan duk akwai jurwaye Ya...

GURBIN IDO

Gurbin ido ba zai zamo ba idaniya Sai mui kwatance don rabauta bai daya Wane mutum inji muttuwa da ake fada Turkashi na san za ku gane gaskiya In ka ga linzami ga Doki ne kawai Wane su kaza kun sani ta Sha wuya Wai ni ake cewa in zo in dafa kai Inji Kantamawi kunji wai don zolaya Ya bani kunyar sai da ma nattsorata Tuba na ke yi Kantamawi gaskiya In banda zuhdu na gingimemen malami Da tawali'un manyan da ke kin duniya Ya ni da dan titibiri mara ganiya Zan kai kamar Garban mu Sarkin Kafiya? Fata na san danshin ku  ko nai azzama Zan zo a shafan kai su bar min dariya Allah ya ba mu ya ta ku ko can lahira Na san ku na kauna ga Khairul Anbiya

GWANIN MAI KOYO

Bismillahi za na tsaro waƙa Ta gwanaye ciki da 'Musan Gayya' Yau ina alfahar da 'Musan Malam' Ya zamanto gwani abin a kiyaya Da ace babu masu koyo tabbas Da gwani ya zamo abin jin kunya Tun ya na ƙanƙani mu ke tatata Ga kafafun sa sunyi ƙwari gaya Na yi murna da ɗalibin yaffini Ni kawai sai na ce da shi Ala raya Ga fa Musa Rufa'i mai albarka Haziƙin ɗalibi maso jin kunya Ya kasance tsatson 'Karin Kundi' ne Ga shi ɗa gun Rufa'i mai tarbiyya In ka koma ta ɓangaren Barnoma To gwanintar jinin su ne zurriyya Rabbana sa ya zam na tsoron na ka Kar ya zamto dugadugan sa su juya Tsarkake zuciyar ka sa ikhlasi Gun tilawa ka sa ya zam ba shi riya Rabbana ƙara ba shi ƙarfin hadda Don ya zamto gwanin da ba bu hamayya Godiya gun Rufa'i jikan Hamza Muqri'i ne a daina ma jayayya Bai da aikin da yawwuce Qur'ani Sa ya cece shi ran da duk za'a tsaya Ba tijarar da taffi yin Qur'ani Don kwa 'Ahlin Ilahu' ne nan dunya Da...

ALLAHU RABA MU DA SAKARCI

Mabiya Blacky Bakin Bawa Ku tuba ku daina munafurci! Bismillah Allah zan fara Kasidata kan yan Faira Ina so ne dai sui lura Su tsira su bar duk shashanci Dubun tsira a wajen Nura Ma'aikin nan Abban Zahra Muhammadu wanda ya je Isra Da alaye har nas da aminci Ina ta kira gun yan Faira Ku bar bautar gunkin Ibra Ku kama Tabaraka don tsira Ku daina Hakikar sakarci Ku san Allah ne mai tsara Dukan lamari in ya jera Baya gajiya ko yayi jira Jiran Ibron yai sassauci Dukan Kassai shi yajjera Hakan sammai kuma ya dora Fa ba shi jiran wani yai gyara Tabaraka Allah Mahalicci Ina kuke ya ku yan Faira A sanda akai sama an jera Ina Ibron ya ke ga fa dara Ku ban amsa ba son zuci Kuna cewa wancan Ibra Halittu shi wai yattsara Mutum ya ke ko ba ku dibara Allahu raba mu da sakarci Idan Allahu kwa ya tsara Nufin shiriya sai yaggyara Idan kwa bata ya zamo qadara Fa za ku zamo a munafurci

ALLAH JIKAN MALAMI MAI QALA HADDASANA

Allah jikan malami mai qala haddasana Sannan ka sa shi makotar Sayyidul Kauni Ya sha wuya gori ka hada batun asali A hakan ya sauke littafai harma Sahihaini Farkon fadan sa da yan ilimin Hakika ne Su ka zam kiransa da Ahmaq zantukan muni An fara dagar da tsagin Qadirawa ne Magana ta Sawi da yai gefen Jalalaini Aka ce a maida shi Ghana wai na haure ne Kuma wai aqidun sa sun sabawa Qur'ani Duk wata kutungwuilar da sun kai ta zamo banza Domin ya na nan da tanyon Jalla Ramhmani Ya rayu kam kuma yai tsufansa mai kyawu Kan burtalin sunna hakaza na Qur'ani Yayinda Bawa na Inyas yayyi banbarma Malam ya fede Hakika tunda tai muni Su ka je wajen wani wai shi Tambari Yabo Ba sa batun kare Manzo Sayyidul kauni Ya fara da'awar nan tun a Bayero ne Darul Hadisi ya koma don matsin tsanani Alhamdulillahi Malam na yi ma barka Da ka furfure kan hadisan da ga Adnani Ya tarbiyar, ya zaburar sannan kwa ya koyar Fanni na ilimin hadisi har da Qur'ani Baiti na Larabci da...