Posts

Showing posts from July, 2022

Mujaddadin Tajwidi

Image
MUJADDADIN TAJWIDI Rabbana ya jikanka Baba Ya uba ga Uwar Habiba Har Kada, Kakisu, Garba, Mujtaba da Karibu babba Sa yana Firdausi ba  kasan ba Sannu Malam mai Shababu Haziki Bawan Wahabu Mai tilawa babu aibu Hadimi ne gun Kitabu Sheikh Ibrahim na Garba Babba Juriya ga yakamata Jarumi mai son karanta Alkitbu cikin nagarta Ba kure kuma babu bata Harafi daya bada kuskure ba Kunga gwarzon masu kwazo Yai kiran jama'a kwa sun zo Sunka amsa mas da bozo Gyara Kurani ko sun zo Allah ya biyaka Jalla Rabba Sanda Kur'ani ya zo shi Hausa duk kowa ya san shi Ya fa zo kan ka'idar shi Ba bu mai barna cikin shi Kuskure mai yi ba ka jiya ba Tafiya sannan ta dora Nan ga manya harda yara Babu mai son ma a gyara Kuskuren furuci da rera Tamkar Hausar mu ba ba'a ba Ba bu mai yin tajjawidi Ba mafurta ba bu maddi Ko sifar harafai da kaidi Ba ga kolo ba bu gaddi Sai dan sauran da bai bace ba Can alif da dari taran nan Sai tamanin tai tsakan nan Rabbi yat turo da wannan Gangaran tajwidi kenan Al...

ALLAH JIƘAN MASOYI WAYE

Image
AMSHI: Allah jiƙan masoyi Waye Don ƙaunar da yai wa Mahye Allah Ƙadiran wa Muridan Wanzajjen da kullum raye Shi zai gaje wannan sarari Mai ilmi Azizu Iyayye In ya kira ka tilas ka je Ba bu cikin mu mai tawaye Yau ya ɗauki daraktan nan Mai hali zubin sufaye Ran Lahadin huɗun Zul-Hijja Ba ciwo fa ran ya kwaranye Hijra na alif da ɗari huɗɗ Sanya ukun ka kan arbaye Daraktanga Nuruddini Mu a rashin sa mun yi hawaye Mui haƙuri mu yi masa murna Domin ya bi Manzo Ɗahye Duk faɗin mashirya ƴan fim Banga salon zubin shi Waye Shi wa'azin cikin fim ɗin sa Zai tsarma a duk halaye Ya nuna cikin tsarin nai Kyawawan halin sa Fiyayye Tasiri na roƙon Allah Har ƙarya da ta gun bokaye Duk fim ɗin sa ka ji hadisai Har yin sallama gun Ɗahye Kyawawan hali na musulmai Ya koya su ba wai ɓoye Ƙaunar Mustapha Baƙuraishe Ya nunawa Ƴan Nanaye Tun rasuwar sa Mamman SK Ban ji rashin da yakkai Waye Shi SK yana yin bege Duk a salo na 'Chori bachaye' Shi kuwa Nura Ɗa gun Almu Duk a zube ya ke ta kwaranye Ya ...