Posts

Showing posts from November, 2021

ƊAN NAWFALU SADAUKIN DATTIJO

DAN NAWFALU SADAUKIN DATTIJO Na shigo bege na Baba Mai yawan bauta ga Rabba Tun ana shirka da gaba Dan uwa ga Khadija Babba Da ga Nawfalu zan yaba ku duba Mai nufin tanyon Ma'aiki Kun ji dattijon saduki Jarumi shi ba shi raki Da ga Nawfalu sannu zaki Yau nazo gaisuwa ga Babba Tun ina yaro na jika Sanda wahyin nan ya sauka Nan ga sirar nan da marka Nai nufin sai nai yabokonka Ga shi alkawaringa ban ware ba Can da daddare gunsa Sallau Malami dattijo hallau Tajiri bai kyau da tallau Ya bide shi ruwa a jallau Malamin Dare mai sani ga Rabba Zan fado da ga nassabar sa Zan tawo har illiminsa Littafan da su ke akansa Har yawan kankan da kansa A ciki ba zan rage kobo ba Ya kasance da na dangi Nan kuraishi yana da tsagi Ga jinin Asadun a dangi Sun kasance ba su wargi Asali ba'a fi su gun tsatso ba Waraƙah sun kai kiransa Shi kwa Naufalu gyatuminsa Ɗan Asad ku biyoni nesa Abdu Uzza ne ubansa Ɗan Ƙusayyu kaza Kilabu Baba Naufalun kuwa ɗan uwa ne Gun Khu...

Rakiyar Wata

Komiyyi farko ƴan uwa Ƙarshensa na nan zakkuwa Kwai zamiya ban sukkuwa A watan da ankai haihuwa Sai mai yawan rai ƴan uwa Wada duk ni ke son zan 'whaɗa' To an riga wani ya faɗa Fa ya na da gaggan banbaɗa Allah ya kaimu baɗin baɗa Ƙaunarsa tai yo ƙaruwa Duk Litinin mui azzumi Don maulidin sa BaHashimi Duk Juma'a mui lazumi Na salatukan sa mu bar ɗumi Begensa sai mui mai yawa Allah ka bar mu da mu da shi Nan duniya har tadda shi Tafkinsa mui arba da shi Ranar da zai mana murmushi Tsira a kan sa ka ƙaruwa