MURMUSHI GA MADUBI
Salatin Manzon mu Annabi Tamkar fara'a ce ga madubi Ka murmusa fuskar ka ka gani Mudubin nai maka da laddabi Ribar sa ga mai yi kwa tai yawa Domin kwa adashi kake zubi Ranar ɗauka tun a duniya Ran tashi ladan ka bi-da-bi Dukkan darajoji da martaba Akwai a salatin sa Annabi Hasken fuska har na zuciya Da kwai a salati idan ka bi Idan ka yi Allahu zai maka A Cikin alfarmar Sa mai Maka Da goma Ta'ala ya ke biya Da kai ɗaya tilo ga Annabi Ko don yiwa kai ma ku yi ma sa Kuma ga shi ibada da anka bi Allah kai tsira ga Annabi Har ma da amincin Ka bi-da-bi Sanyo ahlin na Sa su duka Da sahabbai har ma da ma su bi