Posts

Showing posts from September, 2023

TAMBAYAR WALAKIRI

TAMBAYAR WALAKIRI Bismillah Allah Auwalun kuma Akhiri Shi Baɗini ne shi ya zam kuma Zahiri Tsira aminci kan Masoyi Shugaba Kuma jagabana Mai son mu san alheri Kan tambayar ƙabari na ke son nai batu Bar duk abinda ka ke ka ɗan saurari A Qawa'idi ƙarshen sa za ka duk batun Ga tambayoyin ga jawabin jeri Bawa idan ya mace fa tabbas za su zo A mala'kun da mu ke kira Walakiri Domin a san matsayin Habibi Mustapha Matsayinsa na kan tambayar Walakiri Bayan rufe ka maƙabira kam za su zo Su su biyun nan Munkarun da Nakiri Nan za su tashi mutum cikin ƙabari nasa Sui tambayoyin nan bisa kan tsari Man Rabbuka? Ma dinuka? Sannan su ce Me kaƙƙudurce kan Bashiru Naziri? In har a nan dunya ka na a cikin waɗan- -da su ke ganin girmansa amsar sauri Sai Munkarun har ɗan uwansa su ce da shi Kwanta masoyin Mustapha da sururi Inko ya zamto masu son fifita son Wani Gansami kayin sa zai sha mari   Wai sai ya ce shi ya ji ne a cikin gari Zai kasa amsawa a kayin tsari Nan za ya sha mazga da ƙaton sungumi ...

BARAM-BARAM

BARAM-BARAM Annabi na sonka nake Kana ƙin mai ƙin nake Nai bara'a ba ni sake Izgilancin nan da suke Sun yi zane sunka sake Intanet can sinka fake Dauri anyo Dandarake Mai ƙafafun fanfalake Yau ko hoton nan da suke Ya yi muni kar mu sake Ga tokobi nan a rƙe Wai fa Islam yanda ya ke To Muhammadu sun yi sake Ya fi taurarin falake Kyansa ya wuce duk ku riƙe Kwarji ne ga hasike Sanda Hassan yai kasake Ya ga kyawu kyan gaske Maimakon zambon da ya ke Sai ya hau bege ya dake Darajoji gun sa suke Martabobo shi ya riƙe Hassadar nan duk da ku ke Ba ta tauye yanda ya ke Wanga yaƙi ne da ku ke Ku da Al-ƙahharu ku ke Faɗuwa ce har a tuƙe Ba bu riba duk ku riƙe Duniyar nan ba ku sake Ƙuntata ce har a tuƙe Lahira wuta za'a sake Ƙarƙashin Saƙara a niƙe Izgilancin duk da ku ke Bai na da can wanda ake Ran Badar duk anka sake Rijiya ɗuk anka ɗake Babu wadi don ku fake Koko tsauni har a tuƙe In Ta'ala za ya riƙe Tsanani damƙar sa ta ke Na Samudu da Adu su ke? Ƙaumu Lufin duk ya niƙe Har biranan...

BONE KAN KU

Jafa'i kan ku Denmak ke da Nowe A kan gauƙan da kun kai kui hawawe Ace Manzon da babu kamar s akwata Ku ke wa ba'a fa kun san kunyi wauta Ina zatgin ku zargin bai zaya ba Ina zagin ku zambo ban raga ba Akan ƴanci na furci sun ka yo wai Da farko har da arnan sun ji bawai Ama manyan musulmiya kona oho Fa sai ƴan kasuwa ne sun ka eho Suna Allah wadai kan wanga assha Musulmai hankali duk ya yi tsahi Ina.wai duk ƙasashen masu fetur Musulmin nan cikin su su dinga tur-tur Fa fetur na mu ba shi zuwa ga Denmak Ku bar Dolar ku, Sefa koko Dochmak Kaza dukkan ƙasashen nan na yamma Akan cutar mu kullum su ka yimma Fa ranar duk musulmi sun yi shewa Gama kalmar Ta'ala tai ɗagawa Daɗewa Ali Mazrui ya yi sharyi Akan shi feturi Allah Buwayi, Ya na jibge shi ne gun duk ƙasashan Musulmai koko inda su kai yawa shan Makammin nan da Allah yaffa ba mu A ya zarce su nukiliya a gun mu Musulmi na kiran duk masu ilmi Na sadarwa ku tashi ku dinga ƙaimi Akan radɗi ga arna masu bante Su na yawo kanar tal...

MIFTAHU MABUƊIN ALJANNA

Image
Miftahu Mabuɗin Aljanna Don shi zai buɗe Rilwana Bismillah da sunan Subhana Mai Jinƙai shi ne Rahmana Tsira da aminci su gudana Ga Rasulu fiyayyen man kana Waƙe ne hallau zan tsara Kan keɓantar Abban zahra Bayan dunya daɗa an ɗora A ƙiyama can ma zai nuna Tuta ta Yabo na hannunsa Babban ceto na daman sa Allah sai ya cika zancen Sa Zai bashi ya bashi da zai murna Bayan turkaturkar ceto Al-Muntaqimu ya fuskanto An je gun kowa sai kaito Gwarzon ya cane ku tawo guna Ni ne da ita a bisa tsari Yau Allah ya cika alƙawari Zan cece halittu gun hatsari Sai yai ta kirarin Subhana Rannan zai faɗi ya na sujada Da kirarin kimshe daga Ahada Allahu ya ce ma sa Mahmuda Yau babu ibada ba sauna "Roƙe ni na baka buƙatun ka Kuma cece na bar ma ceton ka Yau ranar nunin girman ka Ga halitu" zancen Subhana Bayan an jingina mizani Allahu Tabaraka Rahmani Ya ware na dama da ƴan hauni Ƴan dama su doso aljanna Nan ne za ai cirko-cirko Sai ga Manzo ya durkako To kun ji fa wanda ake dako Nan zai nuna shi ...

Ya Rabbana raya mana Muhammada

Image
"Ya Rabbana raya mana Muhammada Har dai ya girma yai gudu kamar gada Sannan ya zamto shugaba na duk guda Ka rusa masu ƙin sa har mahassada Sannan ka ba shi ɗaukaka ta sarmada" ----Shaima'u yar uwar Annabi (ASW), mai rainonsa kuma mai ƙaunar sa (RA)

ƘAMSHIN MAJE ARSHI

 Tsira da aminci a gare shi Abban Kulsumu Maje Arshi Bismillah da sunan Zul-Arshi Rahmanu Majiƙan bayin shi Harshe na sanya yai laushi Zan begen Mai kyawun gashi Tsira da aminci a gare shi Baban Zahra'u da Ibrashi Ahli har duk a sahabban shi Haka nan duk mai bin sahun shi A cikin wannan na ɗau ƙusa Zan ƙero sirrin kamshin sa Da gumi nasa wanda ya ke fesa Madarar kamshi na buwayar shi Fa Anas Ɗan Maliku ya furta Yanayin ƙamshin Babban Binta Da ga nesa da zarar ya gifta Fa ake gane dosowar shi Ga Ummu Sulaimin innar sa In ta so miski mai ƙamsa Gashi da gumin sa ta ke kwasa Domin haɗa kamshi mai tashi Mata a Madina su kan samo Mazubi domin in ya zarmo Su tara su aje domin kamo Baki na zare da turaren shi Yara su ka tura don neman Shashi na gumin Manzo Mamman Da kwalabe ne ma na musamman Don kowa ya san ƙamshin shi Da Anas Ɗan Maliku zai ƙaura Ya bada wasiyya da ishara In likkafanin sa kwa an gyara A haɗa da gumin sa maje Arshi In an hada miski da gumin sa Lallai kamshin nan zai nisa S...

MUHAMMADU YA FI KOWA

YA FI KOWA! YA FI KOWA! YA FI KOWA! A yau kuma zan Safa ne har da Marwa Akan duk masu karyar wallafawa Taqiyyar son fiyayyen Annabawa Da bai iya son sa har ya ji ya fi kowa Akwai wasu sun amai sai sunka lashe Mu na nan har jinin mu diga ta ƙarshe A tsarin kare Manzo Ɗan Abashe Da cewa duk halittu ya fi kowa Idan kai ba ka yi to ba mu fili Batu kan martabar jikan Khalili Muhammadu Mujtaba Yayan Aqili Mu na kai har mu koma can kushewa Faɗan nan ba na mai tsoro ba ne ba Idan za kai ka jure duk azaba Anan dunya a can ko duk da riba Fa sai dai ɗan kucaki bai iyawa Idan na tuno guruf ɗin ƴan hakika A shafin Facebook don yaɗa shirka Da daukaka shehinai kan Masu Makka Takaici har hawaye nai zubarwa Idan kun tsuke baki ni ku ji ni Ba zanyi shiru ba ko zan karɓi tsini Takobi, tsitaka mashi biyo ni A tsagin kare Manzo ban gazawa Idan ka ji wanga waƙe kaffusata Munafunci da tsatsa sun yi kanta A ƙoƙon zuciyar ka idan na keta A ƙaunar Mustapha ban ratsa kowa Idan ka ji ka fi son wani kan Muhamman K...

SARKIN SARAKUNAN TAUSHI (Hassan Ɗan Thabit)

Image
Farko da sunan Gwani wannna da yai iska Roƙon da nayyi ka ban ilmi na domin Ka Sannan ka ba ni fasaha yanda zan taka Rawar da ba muguwa ba wajen yabon na Ka Da shi da dukka sahabban Sidi mai Makka Allah Gwani na Muhamman inji kakata Ƙaro dami na salati kan Uban Binta Alai sahabbai da ƴaƴa har da mai bauta Bautar Ta'ala da yai Gano da Ɗanbatta Har masu bin su da kyawu ba su yin shirka Bayan hakan zan bayanin Mai kiɗan taushi Hassanu mai kare Manzon nan Maje Arshi In an taɓa shi ya zam zaryar da ba fashi Zai kai mari har da gwauro don ya wanke shi Hassanu Kam ya rabauce babu ko shakka Kafin zuwan Islama ya zamo gwarzo Harshensa kansakali mai fauce duk zozo Zai sulluɓe su da baitoci ya duddurzo Jinga ake yi da shi gayya idan sun zo Domin ya kare ƙaɓilu tun ana shirka Ana cikin haka sai Manzo ya zo da kira A daina bautar gumaka don a san tsira Arna su kai dandazo har ma su na kyara Ga Shugaba na halittun nan Uban Zahra Hassanu shi ma a loton na cikin harka Sun tattago shi ya je wai don...

WA YAI KAMA TASA DUK BAYI NA RAHMANU?

Image
Wa yai kama tasa duk bayi na Rahmanu Ra'ufu ne da Rahimu jini na Adnanu Bismillah Sarki Gwani Rahimu Rahmanu Ka ba ni himma cikin bege na Ma'munu Tsira hada da aminci kan sa Miftahu Haɗa da albarkatu jinkai na Hannanu Saka ciki alihi har duk sahabbansa Da ma su bin su da kyawu duk cikin kaunu Na ɗauki allo na latarki Ina da nufin Tsaro yabo a wajen suriki na Usmanu Na firgice ni a ƙaunar nan ta Manzon mu Wasu lokutan ma Ina jin na fi majnunu Riba ta begen Rasulullahi ba ta Sa'a Duba ga ƙissa ta Ka'abun nan da Hassanu Yayin da Manzo ya sa neman ruwan jallo Gun Ka'bu bi ni gaba zan ba ka duk kanu Zambon da yai wa Ma'aikin ne ya sanya Hakan An sa a Nemo shi ko da har cikin bunu Sai ɗan uwansa ya je ya sanar da shi halin Da ake ciki a gari halin da yai munu Amma ya ce masa shi Manzon maji ƙai ne Ga yafiya a wajen Bawan na Rahmanu A cikin duhu na dare kafin kiran fajaru Ya je ya kai shi gaban Manzo ya gurfanu Nan ne ya buɗe kasidar nan da tasshara BANISSU'ADU da ...