KARYAR WUSULI

Zancen wusuli ba da tababa ba
Mun yarda karya ce ta mai yin zama

Ba wani tajalli ba fana'i sannan
Balle barin taklif ibadun kenan

Wallahi hanyar nan ta shaidani ce
Ku biyo tafarki in kuna son dace

Duk wanda yai shirka ga Allah Jalla
Sai ya zamo iccen jahannama tallah

Inyasi ko ku sani fa ba Allah ba
Kuma bai fi Manzo gun yawan daraja ba

Na san ka na zagi idan na tuna ma
To shi kwa zagi kari na gaya ma

Allahu dai ne bai abokin tare
Kuma bai kini duk na fada kun shude

In kun ki ji ku sani ba kwa ki gani ba
Ranar shiga Saqara da Lazza duba

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka