Raina Fansar Ka

Ina ƙaunar Miji gun Nana Hafsa

Iyayena da kaina gun ka fansa


A sunan Rabbu Ƙhaliƙu ne na kan sa

Idan zan fara komai don isar Sa


Salat da salami ninninka akan sa

Da rahma har da albarka akan sa


Da mataye ka sa ahlin gidansa

Sahabbai har da masu biyar sahun sa


A bayan nan a yau zan nuna son sa

A waƙen nan idan na bada amsa


Ga mai neman dalilin nuna son sa

Da arna masu batanci akansa


Da fatan za su gane ina na dosa

Gama sam ba su gane kala ta sonsa


Muna ƙaunar sa ne ƙaunar da ke sa

Mu bar komai idan shi za ya nisa



Abu Sufyanu in na tuno batun sa

Da ɗai bai san ba wanda ka so kamar sa


A faɗin duniyar ga iya saninsa

Mutum bai so waninsa ba sam kamar sa


Sahabi ne ana cisgar jikinsa

Ya ce bai son ƙaya fa ta je wajen sa


Mu kan iya bada komai mu a kan sa

Iyaye duk da dangi kansa fansa


Riƙe al'ana ya Umari hadisa

A son sa ku sa dukan komai ƙasansa


Ku so shi ku bi shi ba mu da ɗai kamar sa

Mu kare shi da alayen gidan sa



Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

Ya Rabbana raya mana Muhammada

MU TSARKAKE ALLAH