Mujaddadin Tajwidi

MUJADDADIN TAJWIDI
Rabbana ya jikanka Baba
Ya uba ga Uwar Habiba
Har Kada, Kakisu, Garba,
Mujtaba da Karibu babba
Sa yana Firdausi ba  kasan ba

Sannu Malam mai Shababu
Haziki Bawan Wahabu
Mai tilawa babu aibu
Hadimi ne gun Kitabu
Sheikh Ibrahim na Garba Babba

Juriya ga yakamata
Jarumi mai son karanta
Alkitbu cikin nagarta
Ba kure kuma babu bata
Harafi daya bada kuskure ba

Kunga gwarzon masu kwazo
Yai kiran jama'a kwa sun zo
Sunka amsa mas da bozo
Gyara Kurani ko sun zo
Allah ya biyaka Jalla Rabba

Sanda Kur'ani ya zo shi
Hausa duk kowa ya san shi
Ya fa zo kan ka'idar shi
Ba bu mai barna cikin shi
Kuskure mai yi ba ka jiya ba

Tafiya sannan ta dora
Nan ga manya harda yara
Babu mai son ma a gyara
Kuskuren furuci da rera
Tamkar Hausar mu ba ba'a ba

Ba bu mai yin tajjawidi
Ba mafurta ba bu maddi
Ko sifar harafai da kaidi
Ba ga kolo ba bu gaddi
Sai dan sauran da bai bace ba

Can alif da dari taran nan
Sai tamanin tai tsakan nan
Rabbi yat turo da wannan
Gangaran tajwidi kenan
Allah kai haske ga da na Garba

Dalibai har duk diyansa
Har makota duk ka amsa
Unguwannin kewayen sa
Rabbi yassa duk kiransa
Ya ishe yaro gami da babba



Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka