MURMUSHI GA MADUBI
Salatin Manzon mu Annabi
Tamkar fara'a ce ga madubi
Ka murmusa fuskar ka ka gani
Mudubin nai maka da laddabi
Ribar sa ga mai yi kwa tai yawa
Domin kwa adashi kake zubi
Ranar ɗauka tun a duniya
Ran tashi ladan ka bi-da-bi
Dukkan darajoji da martaba
Akwai a salatin sa Annabi
Hasken fuska har na zuciya
Da kwai a salati idan ka bi
Idan ka yi Allahu zai maka
A Cikin alfarmar Sa mai Maka
Da goma Ta'ala ya ke biya
Da kai ɗaya tilo ga Annabi
Ko don yiwa kai ma ku yi ma sa
Kuma ga shi ibada da anka bi
Allah kai tsira ga Annabi
Har ma da amincin Ka bi-da-bi
Sanyo ahlin na Sa su duka
Da sahabbai har ma da ma su bi
Comments
Post a Comment