BAKI YA YANKA WUYA
YA YANKA WUYA
Na fito kare Ma'aiki
Mustaphan mu na Ummu-Hani
Dukiya har rayuwata
Za ni ba Ɗan Addanani
Babu tsoro babu shakka
Babu mai iya kakkaɓe ni
Yau da kaka anka ƙare
Duk da an fara da rani
Yau hukunci ya yi kyawu
Tunda an yanke bisani
Audu ya yi ɓatan ɓatantan
Babu tarko ba mayani
Babu sauran ƴan tastine
Tunda an rushe ɗayani
Yanzu kogon ma kufai ne
Babu shehin ƴan zamani
Tauna tsakuwa don aya ne
Na ji zancen Dakta Sani
Isgili an kaiwa Nuru
Mujtaba Kakan Husaini
Rabbana ba zai bari ba
Duba Hijri cikin Ƙurani
"Mun isar maka isgilin su"
Kunji Jalla ya na bayani
Rabbu na kishin AbinSa
Zai yi damƙar ne da tsanani
Jinjina Ɗan Sarki Yola
Malami kuma mai sukuni
Ga hukunci ga sarauta
Ga tilawar Al-ƙurani
Maluman mu gaba ɗayan su
Sun rawa ta gani da nuni
Rabbana ya biya ku sannan
Yai hanin duk ma su muni
Zai saka a cikin biɗar ku
Sanda anka aje ma'auni
Sai salati har salami
Kan sa jikan Addanani
Alihi da dukan sahabbai
Tabi'ai har Al-Bunani
Ni Na'Annabi ne Muhammad
Banbaɗon Kakan Husaini
Gomiya biyu ɗai ka ɗora
Kan Jumadar Lawwalaini
Shekara ta alif ɗari huɗu
Arba'in da huɗun bisani
Shabiyar ga watan Disemba
Álifain ashirin biyo ni
Sai ka ƙara biyun ka gefe
Haihuwar Ruhul-Amani
Godiya a gare Shi Allah
Mai Jiɓintar salihaini
Comments
Post a Comment