Rakiyar Wata

Komiyyi farko ƴan uwa
Ƙarshensa na nan zakkuwa
Kwai zamiya ban sukkuwa
A watan da ankai haihuwa
Sai mai yawan rai ƴan uwa

Wada duk ni ke son zan 'whaɗa'
To an riga wani ya faɗa
Fa ya na da gaggan banbaɗa
Allah ya kaimu baɗin baɗa
Ƙaunarsa tai yo ƙaruwa

Duk Litinin mui azzumi
Don maulidin sa BaHashimi
Duk Juma'a mui lazumi
Na salatukan sa mu bar ɗumi
Begensa sai mui mai yawa

Allah ka bar mu da mu da shi
Nan duniya har tadda shi
Tafkinsa mui arba da shi
Ranar da zai mana murmushi
Tsira a kan sa ka ƙaruwa

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

Ya Rabbana raya mana Muhammada

MU TSARKAKE ALLAH