ƊAN NAWFALU SADAUKIN DATTIJO

DAN NAWFALU SADAUKIN DATTIJO

Na shigo bege na Baba
Mai yawan bauta ga Rabba
Tun ana shirka da gaba
Dan uwa ga Khadija Babba
Da ga Nawfalu zan yaba ku duba

Mai nufin tanyon Ma'aiki
Kun ji dattijon saduki
Jarumi shi ba shi raki
Da ga Nawfalu sannu zaki
Yau nazo gaisuwa ga Babba

Tun ina yaro na jika
Sanda wahyin nan ya sauka
Nan ga sirar nan da marka
Nai nufin sai nai yabokonka
Ga shi alkawaringa ban ware ba

Can da daddare gunsa Sallau
Malami dattijo hallau
Tajiri bai kyau da tallau
Ya bide shi ruwa a jallau
Malamin Dare mai sani ga Rabba

Zan fado da ga nassabar sa
Zan tawo har illiminsa
Littafan da su ke akansa
Har yawan kankan da kansa
A ciki ba zan rage kobo ba

Ya kasance da na dangi
Nan kuraishi yana da tsagi
Ga jinin Asadun a dangi
Sun kasance ba su wargi
Asali ba'a fi su gun tsatso ba

Waraƙah sun kai kiransa
Shi kwa Naufalu gyatuminsa
Ɗan Asad ku biyoni nesa
Abdu Uzza ne ubansa
Ɗan Ƙusayyu kaza Kilabu Baba

Naufalun kuwa ɗan uwa ne
Gun Khuwaild don ku gane
Gun Ma'aiki sirriki ne
Kunga Kakan muminai ne
Abba ga Khadija je ka duba

Sun kasance ma su zuhdu
Ba su zarmewa hududu
Ɓurɓushin ilimin Yahudu
Ya zame mu su ne ya mudu
Don awon Islamu ba ɓata ba

Shi da wassu abokanan sa
Su uku su ka nemi amsa
Kan abin bautar garinsa
Sun ka ce sun daina binsa
Za su je nema ba sa sake ba

"Ya gumakan nan na dutse
Ko idanu ba su runtse
In kwa tankwa za ka matse
Ko ka ɗau adda ka gimtse?
Wanga ba hanyar Khalil ba ce ba!"

Waraƙah ne shi da Zaidu
Ai mahaifi gun Sa'idu
Ɗan Sa'adatu Ƙassu su du
Sun haɗu sun ɗaura sirdu
Neman hasken da ba duhu ba

Waraƙah har Zaidu nasa
Har zuwa Sham sunka nisa
Tambayar su ka sami amsa
Annabin Ƙarshe nufinsa
Zai fito ne Makka ba musu ba

Nan kwa Zaidu ya gasgata shi
Yahhaɗo ƴan komatsan shi
Don zuwa birnin Ƙuraishi
Annabin kuwa zai jirashi
Bai kuma duƙawa gingirin ba

Inda Allah yai nufinsa
Tun gabanin ma ya gansa
Rabbana yakkarɓi ransa
Ba shi bautar duk wanin sa
Ɗan uwan Khaɗɗabi bai sake ba

Ɗa ga Naufal ya bi Taura
Don cikin ankai bushara
Da zuwan Mahmudu Nura
Littafai tari ya tara
Bai sake zuwa gaban Hubal ba

Ɗan Sa'adatu Ƙassu shi ko
Ya jira har anka aiko
Mustaphan da su kai ta dako
Ya riƙa sam ba bu tsaiko
Ya yi imanin da ba giri ba

Shi kwa Warƙatu har ya tsufa
Ya makance har ya dafa
Zuciya tasa har da saifa
Yayi imani tunin fa
Sai Khadija ta ce ya zo ya duba

Waraƙatu shi yai dabara
Gun haɗin aurensa Nura
Shi da Dijatu mai bushara
Sanda Maisara yaɓɓurara
Girgijen da ya ke rufa ga Babba

Maisara duk yai bayani
Wanda Nastura ya nuni
Har yahidun nan na raini
Wanda yai ƙarin bayani
Kan risalar Mahe bai rage ba

Sanda Waraƙa yajji wannan
Yai tunanin Annabin nan
Da ya tsufa ya na jiran nan
Gashi nan jika ga Adnan
Shauƙin da yayo ba zan faɗi ba

Ya sani ba wanda ke da
Wanga baiwa sai waɗanda
Rabbi zai zaɓa ya bada
Dukkanin saƙon ibada
Gun mutane kunji ba musu ba

Mustapha ko ya kasance
Duk ya na halwa a duce
Don ya na bautar Fitattace
Wattaran Jibrilu yacce:
"Yi karatu ba da gargada ba"

Annabin mu yaba shi amsa:
"Ban karatu tun a nesa"
Yai musayar zantuƙan sa
Sai ya ce iqra' a ƙissa
Ƙur'an duba ba kai kure ba

Mujtaba ya je gidan shi
Gunta Dije uwar gidan shi
Har ya na ta: a lulluɓe shi
Sai tace masa Jalla Mai shi
Ba zai yashe shi duniya ba

Sai ta kai shi ga ɗa na Naufal
Mai tulin ilminga falfal
Yai batu nasa ya ga tamfal
Jibril mai fiffike fal
Kunga ɗan saƙon Kalimu Babba

Yai bayanin wanga harka
Har batun fisshe shi Makka
Har gumurzun nan da shirka
"Nayi niyyar taimakon ka
Wanda ban taɓa yin sa duniya ba"

"Yanzu za'a fitar da ni wai
Nan ga Ɗaki?" ya jji bawai
"Tun a zamunna ka waiwai
Ka ga zancen ba bu waiwai
Gaskiya ba'a barta ta sake ba"

"Babu wanda ya zo da tamkar
Wanga saƙo sai su far mar
Ko kisa koko su cutar
Muminai ko an azabtar
Ba irin wahalar da ba su jiya ba"

Nan fa Waraƙa yai shahada
Nanga mai Tutar Hamida
Tun gabanin ma a ida
Jefa wahyi gunsa Abda
Muminin bai riski yekuwar ba

Don wata biyu ne gabanin
'Ƙum fa anzir' binciƙa min
Yai wafati kunji domin
Rabbi baiyi nufinsa samin
Jin kiran Manzon da yai jira ba

Rabbana Sarkin karamci
Shi ya ke dukkan tukuici
Mustapha ya ganshi barci
Can a aljannar aminci
Jalla bai wofanta Warƙatun ba

Ya sako kaya na iko
Ai farare ko ko roko
Harda haske tunda farko
Ya yi imani da dako
Ba shi bauta gun Manata duba

Ni ina ƙaunar sa Waraƙa
Har ina begen haƙiƙa
In na ganshi kwa za ni duƙa
Don a tarihi na leƙa
Shi ya fara biya ga Ɗan Suwaiba

Ya kasance ne sahabi
Ya ga Annabi kana ya bi
Dukkanin saƙon Habibi
Ka ga wannan inka dubi
Ya zamo a cikin sahabu Babba

Rabbi gafarta Wuraiƙa
Ɗa ga Naufalu ƙam haƙiƙa
Yayi dace kunga haƙƙa
Ya kasance mai zalaƙa
Tunda bai hurwa gaban Hubal ba

Godiya ga Ubangina
Shi ya sauƙaƙa lammura na
Nayyi begen ɗan uwana
Mumini Waraƙa nufina
Don kwa ban yi zaton fa zan iya ba

Nan na ke ajiye rubutu
Sanda ankai assalatu
Safiya ce ma ta Sabtu
Shabiyar ga Rabi na ukhtu
Forteen kuma forty three ku duba

Sai salatin Sidi Babba
Sa iyalai har sahaba
Ko guda ba zan cire ba
Har da ma su biyar su duba
Har ƙiyama ran da za'a tarba




Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka