Maraba da Masoya Waƙoƙin Yabon Manzo ASW
Assalamu alaikum. Barkanku da shigowa wannan shafi mai albarka na yabon Fiyayyen Halittun Allah ASW. Za mu dinga kawo muku rubutattun ƙasidun yabon Manzo waɗanda aka tsara a tsanaƙe don kaucewa salon yabon da Annabi sam baya farin ciki da su da mu ke ji su na yawo a gari.
Idan zaka yabi Annabi ASW amma kuma ka taɓa martabar wani Annabin ko kuma ka faɗi abinda sam bai dace ba a haƙƙim shi Shugaba ASW, to sam Annabi ba zai karɓi wannan a matsayin yabo ba sai dai zambo.
Allah mu ƙe roƙon da ya yi mana jagora kada mu zarme ko kuma mu tauye ɗaya daga martabobin Manzo ASW.
Sannan mun ɗau ɗamarar kare Manzo da ga dukkan wani zambo ko xane ko eani furuci da wasu maƙiya Musulunci ke yi a duk sanda su ka aikata hakan. Wannan alƙawari ne mu ka ɗauka sai dai fatan Allah ya ba mu damar saukewa lafiya.
Mu na ƙara yi muku maraba lale da fatan za ku dinga yin sharhi a wajen da aka ware domin yin sharhi domin mu ƙara samun ƙwarin gwuiwar wallafa wasu sabbin ƙasidu yabo, tarihi,, ko bada kariya ga Manzo ASW.
Mun gode ƙwarai Allah ya ƙaraana ƙaunar ManzonSa ASW.
Comments
Post a Comment