Badaɗina

Badaɗina Ma'aiki Sidi Ahmad
Uban Abdullah Manzona Muhammad

Da sonka na kwan da shi ne za na tashi
A kullum zan yabon nan babu fashi

Ina koyi da Hassan shugabanmu
A baitocin da yaiwa Annabinmu:

"Kamar kyawunka babu idon da yagga
A kyawu ka wuce waccan da wagga

Fa babu macen da tahhaifo shigenka
Kamar dai ma nace kai kayyi kanka

Da an haifoka tas sam babu aibu
Kamar haka nan kaso Manzo Habibu"

Na kan shiga ɗimuwa in an faɗeka
Da shauƙi wanda nasan baida tamka

Idanu na cika tambam da ƙwalla
Akan begenka ya Manzo na Allah

Kusanci ne nake so nan gabanka
A ba sallah gareni bare fa zakka

Ina ɗan sujjada sai ɗan salati
A sani maƙotaka don Rabbu Zati

A lamuncen na zam wani hadiminka
Da in ka cire su takalma na ɗauka

Ina tafiya a bayan Sidi namu
Idan ya sha ya ban ni ne da  kamu

Idan ya cire sahu nasa ni na taka
Kamar Bila fa bawan nan na Makka

Ina roƙonka Allah don isarka
Acan Firdausi kaini ga Annabinka

Gama ni duniyar nan ban da buri
Da yawwuce lahirata nai sururi

Idan ka ce matsona nan zo ka zauna
Mayafin nan rufa min shi jikina

Inai masa sallama harma salati
Abul-Ƙasim, Ruƙayya harda Fati

Na'Annabi ne masoyin nan gareka
A ɗa gun Tanko jikan Tanko naka

Fa tarihin da nai don kattabata
A hijra ga ta nan na anbatota

Ta fourteen-fourty sai uku ce ta ƙari
Safar ya kai bakwai mako na fari

Badaɗina guda kaine Rasulu
A baitocin da nai ai min ƙabulu

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka