DABI'UN GIRMA

Gatanan ku zauna ku jita
Wakar yabo ce na yi ta
Kan jagaban duk halitta
Halinsa ne zan rubuta
Duk da sanin da nai ya ƙaranta

Ya shugaban duk halittu
Na Khadija Abba ga Bintu
In har ka na son mu jitu
To ka fito ka so Ɗa na Shitu
Kyan akhlaku an bashi tuta

Nai jinjina har da godo
Gun Rabbana nawa dodo
Dunyarga Shi zai yi gado
Sannan matattu ya tado
Ranar nuna Gwarzon halitta

Kai sallama har salati
Gun Hamidan mai kanati
Masanin cikar naka Zati
Har ahlihi har banati
A ciki har ka sanya da Binta

Begenka zai sa na zautu
Ya zanyi ne in kusantu
Ga ba karatu rubutu
A fagen yabon banda hutu
Koda zan jiki yajjigata

Na tashi kuka na ke yi
Ihu na ke harda wiyi
Na rassa ya za na ma yi
Kaunarka Mahmudu Mahyi
Kar fa ta zam silar hallakata

Ya mai dabi'u na girma
Aiko ka yai don ka cimma
Wannan batu ya yi shi ma
Halayensa Qur'an ka kama
Ko can ba shi karya da mita

Ko Jalla ma yai yabonsa
Kan ɗaukakar lammarinsa
Da makarimun yai batunsa
Farkon Noon idan dai ka fansa
Aya tahhudun fassarata

Ni Jalla zan so na koya
A batun da yaiwo a aya
Wada nai batu nan a baya
Halayensa yau zan kidanya
Ya Allah ka karan fahimta

Daga A'isha ma uwata
Yayinda an tambayeta
Kan duk ta'adun mijinta
Amsarta ta dunkuleta
Ai Kur'ani in ka fahimta

Wannan ta'adu na girma
Gun Shugaba babu dama
Su zan faɗo yan kaɗan ma
Sai gani sam banda himma
Allah shi fa zai ba ni gata

Mun san shi ango na Assha
Tun fil azal ba shi assha
Ga tattali ba bushasha
Mai hankali ba shi fahsha
Kan kyawun hali ya yi rata

Kunyarsa wane budurwa
Da rikon amana ga kowa
Kyauta ko shi ne fa baiwa
Danginsa ba ya zubarwa
Harda makotaka har aminta

Da yana a tsumma na goyo
Da Banu Sa'ad sunka yayo
Ya nuna hali na koyo
Mamakin Halima da tayyo
Ta yayo gaban duk halitta

In zata shashe su mama
Sam ba shi nunin zalama
Wasu lokutan ba shi sha ma
Na lura a kullum Halima
Mai rainon da ba dai kamarta

Ba ya  faɗa tun azal shi
Fara'a gare shi da mur'shi
Ba'a gane ma yai fushi shi
A guminsa domin da kamshi
Har Ɗan Goma sun yi shi mata

Kyan zuciya ga zumunci
Bai yin fushi ko ko kunci
Wautar mutum ko ko naci
Ba su sa shi rai nai ya ɓaci
Shi ne maganin dukka cuta

Bai yin ta bauta ga gunki
Bai ayyukan nan na shirki
Bai  shan giya ma Ma'aiki
Bai yin sa mugu na aiki
Tutar godiya zai rikota

Matsalar waninsa ya ɗauka
Zai lamuni yabbiyaka
Ko baida shi sai  ya dauka
Da sun samu shi zai kiraka
Kunji uba ga duk mai wadata

Mara lafiya za ya gaisar
Gun gayyata sai ya amsar
Yara kanana ya gaisar
Duk mai bukata ya gamsar
Sannu Rasulu mai son zumunta

Duk duniya ba kamarsa
Gun kyan hali ba irinsa
Mai tausayi ne na Hafsa
Koda ga dabbar hawansa
Manzo ba ya son ai mugunta

A kasuwa ba shi ihu
Siffarsa ce tun a lauhu
Taushin hali ba shi lahhu
Kuma kamili ba shi laghu
Zan fansheka ni da uwata

Bai ji da kai ko ko izza
Shi ne jakadan Mu'izza
Mai tausayi har ga kaza
Washin wuka kar a durza
Ya jinkai ga dukkan halitta

Wani ya shigo yai fitsari
Farfajiyar nan ta zikri
Manzo ko yai massa uzri
Gugar ruwa yayyi amri
Sannan yai hani kar a cuta

In banda shi mai mukamai
Fa abin yabon nan a sammai
Da kasar fa ba masu cimmai
Hakurinsa ya tara dammai
Ni fansarka ce rayuwata

In yai batu zaiyi kari
Kan sannu bai yi da sauri
Harshensa sam babu kudri
Fa Fasihu ne kam Naziri
Mai kyawun jiki ga nagarta

Zan sallama nan na huta
Wakarga ni ne na yi ta
Na'Rasulu mai son ku ji ta
Ga sallama har salata
Kan Mahmudu Abba ga Binta

Rambazzu ne Mazu-mazu
Ɗaba-Ɗaba Bawan Mu'izzu
Mai sujjada gun Azizu
Ango wajen Nana Dizu
Karbi yabonga don arzikinta

Hjira tana dai alif ne
Da dari hudu arba'in ne
Karo uku don su gane
A Muharramun yai rabi ne
Tarihinta don kar a manta

Allahu yai rantsuwa dai
Ya jaddada tunda saidai
Ya ce kana kan ta'adai
Duk ba na Allahu waddai
Mai khulukun azhimun da gata

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka