MU TSARKAKE ALLAH
Ku tsarkake Allah dai ku dawo ga gaskiya
Ka dauki batun nan in ko ka ki shi sai wuya
Ina tsarkake Allah da siffar da sun masa
Su na kirkirar karya ga Sarki na duniya
Fa Allah guda ne ba uba bai da ko ɗiya
Kini baida shi Allahu ne Kwal guda ɗaya
Ina mai hakika mai kiran kansa wahidun
Tuno dulmiyar Fir'auna kogi na Maliya
A yayinda yacce wai azo har a yi masa
Fa bauta a kyale Rabbu sarki guda daya
Kadaita ta Allah ba mu shakkar ta kun sani
Ina yan hakika masu kagenga yan tsiya
Ku ce la sharika lahu a suna da ma sifa
Da duk ayyukan Allahu ya Mai Dawainiya
A Al'arshi Allah ya fa daidaita kun jiya
Irin yadda yaddace da zatinsa shi daya
Kace wai akwai Allah cikin dukkanin jiki
Tajallin da kai zance fa karya ta yan giya
Fa ba bu abin bauta da gaske kamar huwa
Huwallahu Al-hayyu fa Sarkin da yattsaya
Idan zaka shekara yin ibada cikin duhu
Na halwa ka san ba za ka zam Rabbu ko daya
A babu wusuli ba fana'i
fa ko daya
Ana yaudarar yara da daidai da daidaya
Su kan fara sambatu na sabo ga Mai Duka
Abun ba bu kyawu ji ka daure ka dan jiya
Ina sunka samo wanga shirme na yan tsiya?
Cikin wanga addini ku zo na yi tambaya
Tafarki hanifi ne na bautar Ubangiji
Da sam ba bu shirka sai fa bautar shi Shi daya
Badadi na Allah ya kirawomu mu duka
Ya ce mu musulmi ne fa sam ba musulmiya
A yau ga akidun yan hakikarga sun yawa
Su na jefa rudani su na samu shan wuya
Alaihi salatullahi summa salamuhu
Salati na Barhama ku na yin sa ba wuya
A yau shi ku ke dauka ku kai can ku ma aje
Zuwa inda Allah ba shi maisheshi ko daya
Buraima mutum ne ba bu karya cikin batun
Idan ka musa to ka fa kaucewa gaskiya
"Fa inniya Abdullahi" ta shafe duk batun
Da duk ɗan hakika zai yi wato musulmiya
Fa Barhama yace son Ma'aikin mu Ahmadu
Da shi ya ka tunkawo da fahri a duniya
Ina kunka samo fita Shehinku kan Nabi
Da Allahu Wutri ai Gwanin nan guda daya?
Fa subhana Allah kan kazantar da sun fadi
Idan za ka damke su ka sanya ni wariya
Alaihi salatullahi summa salamuhu
Da alai abokan Sidi Raino na sadiya
Alaihi salatullahi summa salamuhu
Ka sa ma su tauhidi da ba shirki ko daya
Alaihi salatullahi summa salamuhu
Ka shiryar da ƴan Faira-Hakika ga gaskiya
Idan sunki ya Allah fa kaine kawai da su
Da mulki da karfi na ka ne duk gaba daya
Comments
Post a Comment