BARAM-BARAM
Annabi na sonka nake
Kana ƙin mai ƙin nake
Nai bara'a ba ni sake
Izgilancin nan da suke
Sun yi zane sunka sake
Intanet can sinka fake
Dauri anyo Dandarake
Mai ƙafafun fanfalake
Yau ko hoton nan da suke
Ya yi muni kar mu sake
Ga tokobi nan a rƙe
Wai fa Islam yanda ya ke
To Muhammadu sun yi sake
Ya fi taurarin falake
Kyansa ya wuce duk ku riƙe
Kwarji ne ga hasike
Sanda Hassan yai kasake
Ya ga kyawu kyan gaske
Maimakon zambon da ya ke
Sai ya hau bege ya dake
Darajoji gun sa suke
Martabobo shi ya riƙe
Hassadar nan duk da ku ke
Ba ta tauye yanda ya ke
Wanga yaƙi ne da ku ke
Ku da Al-ƙahharu ku ke
Faɗuwa ce har a tuƙe
Ba bu riba duk ku riƙe
Duniyar nan ba ku sake
Ƙuntata ce har a tuƙe
Lahira wuta za'a sake
Ƙarƙashin Saƙara a niƙe
Izgilancin duk da ku ke
Bai na da can wanda ake
Ran Badar duk anka sake
Rijiya ɗuk anka ɗake
Babu wadi don ku fake
Koko tsauni har a tuƙe
In Ta'ala za ya riƙe
Tsanani damƙar sa ta ke
Na Samudu da Adu su ke?
Ƙaumu Lufin duk ya niƙe
Har biranan nan da su ke
Sai alamu kai a sake
To faɗan da Ilahu ke ke
Ni bara'a ce fa na ke
In fa Manzo an ka tiƙe
Rabbana sam ba shi sake
Ma'idah Allahu ya ke:
Gun mutun silken sa ya ke
Can Bara'a zo ka riƙe
Tai bayani kan su cike
Masu cutarwar da su ke
Kam sa duk wuta za'a bake
Ai da sannu fa don ku tiƙe
Za ku san zancen da nake
Can a ƙarshen Hijri na ke
Son ma kawo har a tuƙe:
"Mun isar ma kar ka sake
Izgilancin duk da suke
Masu shirkar nan da suke
Za su san kam yanda na ke
Mun sani zancen da suke
Za ya sa ƙunci ka dake
Tasbihi, sujada ka riƙe
Har ka komo inda mu ke"
Jalla na san ba ka sake
Gyangyaɗi kai ba shi riƙe
To Muhammadu na ka yake
Na sani kishin sa kake
Yau muƙaman nan da ya ke
Ga fa kafircin da suke
Rabbi nuna kan na fake
Yanda duk ƙudirar ka take
Jalla gaggawa fa na ke
Na sani dakon su kake
Wanga talala da keke
Wata rana za ka riƙe
Na yi kuka har ma tuƙe
Don takaicin nan da nake
Ba takobi don na riƙe
Ba kwari kuma babu bake
Sai fa alƙalami na riƙe
Ni fa koyin nan da nake
Gun su Hassan kan ya fake
Har su Sinhaji da ya ke:
"jalla Sarki son ka nake
Ayyukana don ka nake"
Shi fa gurbi yanda ya ke
Ba ido ne kar ku sake
Na yi koyi ne ku sake
Don ba zan kai yanda suke
To a ƙarshe kan na tuƙe
Ga fa fatan nan da nake
Sa bala'i kan su sake
Don gidajen nasu niƙe
Har musibu ba yanke
Duk a sasannin da su ke
Rabbana roƙon ka na ke
Sa Zabaniya masu fike
Sui dirango duk faɗake
Kan dukan arnan su niƙe
Wanga zancen nan da nake
Bai buwayar yanda ka ke
.
In ko har shiryar su kake
Zuciya hannunka take
In fushin ka ya zo ka riƙe
Nai bara'a ba ni sake
Ya Muhammadu son ka na ke
Kana ƙin mai ƙin na ke
Rayuwa fansarka take
Har iyaye nawa suke
Duk kumatu na a jiƙie
Alƙalam ɗai ni na riƙe
Wanga ɗan waƙen da na ke
Sa ya zam kuɓutar mu ya ke
Ban da ƙarfin nan da ake
Kai hari koko a cake
Alƙalam shi kam na riƙe
Zan yaƙin har na fake
Ban siyan kayam da suke
Tanɗe-tanɗen nan da suke
Tunda dai bautar da su ke
Dukiya ce ba su sake
in ko har mun daina sake
Zai zamo karya su mu ke
Duk musulmiya anyi sake
Sai fa barci ba faɗake
Ba ƙasa ɗai ta mu d ake
Yanke hurɗa gun su ta ke
Mimbari huɗubar da ake
Sun cane zagin su ake
Wai a daina sun fa fake
Tunzurawa wai fa ake
Mustapha manzo fa ya ke
Ya yi zancen da na ke
yau hadisan nan da nake
Yin karatun na fa riƙe
Ga yawa tarin mu ya ke
Babu ƙarfi ɗai da mu ke
Tsintsiya taron mu ya ke
Babu ɗai sharar da mu ke
Ga dalilam yanda suke
Wanga ƙasƙancin da mu ke
Rayuwa burinta muke
Muttuwa tsoronta muke
Yaushe barcin zai faɗake
Don mu san izzar da mu ke
Koko sai Mahdin da ake
Yin kira ya zo mu sake?
Ya Muhammadu son ka nake
Kana ƙim mai ƙin ka na ke
Ya fi rana ya fi wata
Ya fi taurarin falake
Ya fi Yusufu har Balke
Kwarjin kyawunsa ya ke
Ba ma kusa yanda ya ke
Sai ka ce shi kan sa ya ke
Isgilancin duk da su ke
Muntaqim na nan a faɗake
Sai salatin nan da kake
Kai ta yi masa ba yanke
************************
Na'Annabi Tanko Bala Gabari
3/R.Auwal/1429 (AH)
11/3/2008
Digitalized on:12/9/2019
=26/ Safar/1445
Comments
Post a Comment