MAWADDAH
In kana jin fushi da anbaci Zahra
Ko mijinta da Ƴan Tagwayen Yara
Tofa malam ka je ka sauya dabara
Don kwa tsatsa a zuciya ka tara
Ya kamata mu saura duk kan tsari
Don ƙiyayyar da kai da mai tattaki
Kar ta sanya ka yin fushi da Ma'aiki
Bai buƙatar kuɗin ku ko alkaki
Sai mawaddah ga Ƴan Gida mai Tsarki
Suratush-Shura je ka sumnin fari
In watan haihuwarsa ma ya kama
Babu kai ba faɗa da tada husuma
Ƙungiyar ka daban da ta su kwa suma
Za su ce baka son Uba gun Umma
Shi fa Manzon mu ne Bashiri-Naziri
To batu ne ake na ƙaunar Sidi
Bugi ƙaimi ka sake tamke sirdi
Tafiyar nan shigo ciki ba ƙaidi
Bisa tsari kuje wajen Maulidi
Inda hali ku shafa ma bandiri
Comments
Post a Comment