ƊAN HAƘIƘA KA HALAKA

Dan hakika ka halaka
Mulhidi ne kar ku sake

Ya ki bin tauhidi yana
Zantukan sabon da ya ke

Rabbu ba zai barku haka
Ayyukan shirka da kuke

Ya cane komai da ya ke
Duniya wai rabbu ya ke

Ka ga soko dan wahala
Hankalinka ina ya fake

Ba abin bauta dunya
Sai Ilahu fa kar ku sake

Annabin karshen dunya
Mustapha ManzonSa ya ke

Babu laifi mai wahala
Da ya kai shirkar da su ke

Kunga Inyas bawa ne
Anbaton Manzonsa ya ke

Duk yawan zikrin da kake
Sarmadan bawa fa ka ke

Ba wusuli babu fana'
Zantukan karyar da kuke

"Duk abinda ya bar shari'a
Ba tafarkin nan ba ya ke"

Annabin Rahmar mu daɗa
To gaban fa waninsa ya ke

Zantukan Abdul Inyas
Har ga yau rudani su ke

Mustapha Manzon mu yake
Rayuka fansarsa mu ke

Babu shaidanin da mu ke
Sauna in zancen sa ake

Ya kamata ku tuba ku san
Annabin ma ta fa fake

Sanda duk Manzon ka taɓa
Mai gidanka fa za mu dake

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka