INA SON MUSTAPHA ALAI DA SAHBA
INA SON MUSTAPHA ALAI DA SAHBA
Ina son Mustapha Alai da sahba
Da matayenSa tsarkaka na duba
Da masu biyar su ba zan rarrabe ba
Tsare ni da ƙin su ya Allahu Rabba
Inai muku aɗdu'a ya Sabiqoona
Na Lansaru da ma na Muhajiruna
Gwarazan nan na Badru da kau Hunaina
Shahidan nan na Uhdu ba zan bari ba
A wane ni da zan shiga zantukan ku
Da Allah yaccane ya ma jiƙannku
A saɓanin da yaffita nan cikin ku
Fa ba ni da ɓangare balle na gaba
Cikin nan na su zaɓaɓɓunga goma
Da Ahlu Badar da Uhdu sunada himma
Da masu mubaya'ar nan masu girma
Fa yardaddu su ke gun Jalla Babba
Ilahu da kanSa yazzaɓe su jumla
Ga Manzo duk ciki ba mai fa illa
A Attaura sifar su kaza Lijila
Kira mai ƙin su arne ba da wai ba
Gafuru jiƙan waɗannan ƴan uwan mu
A imani fa su suka sha gaban mu
Ka yaye dukka gilli zuciyar mu
Ra'ufu Rahimu amsa don Suwaiba
Comments
Post a Comment