BEGENKA HAMIDU

Allah ina kauna a gun Manzona
Sanya ya so ni da dukkanin dangina
Da dukan masoya ma su jin begena
Sa duk musulmi ban rage kowa ba

Kaunarka Ahmadu ta cika min zuci
Ta ratsa loko sakuna duk ta ci
Ta bar ni kullum ni da kukan zuci
Allahu don kaunar ka shafe zunubba

Na so ace na zo a tawagar Habsha
Da su kai kidan nan wanda har Nanasha
Ta fake a bayan na ka kallo ta sha
Da na yi alfaharin da ba karami ba

To yanzu zamunnan mu sun banbanta
Sai dai ina begenka Baban Binta
Kullum ya na kone da zuci da hanta
Allah ka kai shi gaban sa ba don ni ba

In nai salati gunka na san kaji
Duk sanda nai dai Rabbi zai yi Odoji
Zai ba ni lada goma ba wani canji
Sallu alaihi wa sallimu ba wai ba

Zan je ziyara Dausayin Aljanna
Raudha na ke so don su ganka idona
Kamshi na shabbakin ka ne burina
Allah ka horen kar na kau ban je ba

In na ji sunan ka na kan shiga hali
Hali na jazaba ga shi ba ni da hali
Inje ziyarar dan uwa ga Akili
Manzo mijin Dija Uban Zainaba

Duk masu begen Mustapha na so ku
Na so ku na so dukkanin mai son ku
Sannan ina koyi da dukka salon ku
Koyo na ke yi tunda ni ban kai ba

Kaunarka Hamidu ta game shi jikina
Ta huda fata har zuwa bargona
Begen ka shi ya zamo cikar burina
Allah Ka sa ba don ace nai nai ba

Sallu alaihi wa sallimu taslima
Har ahlu har sahbai na Baban Umma
Wato Ma'aiki Garkuwar al'umma
Har masu bege ban cire kowa ba



Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka