Bushararru Goma

Bismillah zan jero sahabbai goma
Da akai bushara kan rabo mai girma

Allahu ke unguo da kaine mai rabo
Watao Ma'aiki ko ka ce masa Shayabo

Shi yai rabon aljanna gun wasu sabiqoon
Su har guda goma kuce musu muttaqoon

Acikin hadisin ya fade su daki-daki
Domin zuwa kabarin su zan tattaki

Su Abubakar da Umar da Zunnuraini
Usmanu sai Zaki uban su Husaini

Da Zubairu Dalha sai ka sa Dan Aufi
Sai Dan Abi Waqqas Sa'ad mai karfi

Da Abu Ubaidata sai Sa'eed Dan Zaidu
Na wajen Wuraiqata kunji yan tauhidu

Su ne fa farkon muminan doron kasa
Da Rasulu yai shela ya zam sun amsa

Allah dubun tsira a gun Al-Mujtaba
Yardar ka karo kan sahabbai yan gaba

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka