HAIHUWAR DAN SUWAIBA

Bismillah jalla Rabba
Yau batun nan zani duba
Samuwar Manzonga Babba
Ɗan Kinanata Ɗan Kilaba
Mustapha na Khadija Babba
Yau abin ba ƙanƙani ba ne ba

Haihuwar da gun Suwaiba
Duniyar nana ba taɓa ba
Anga manyan al'ajubba
Duniya ta sami Babba
Lale da zuwan ka ya na Garba

Tunda Allah yai halittar
Adamun tun babu matar
Yassako haskenga tartar
Kan tsatson haularsa totar
Koda ɗai ba'a sami tuntuɓe ba

Yattawo ya zuwa ga Shisu
Har ga Nuhu zuwa wasunsu
Mudrika har illiyasu
Ga Kinanata ga Kuraisu
Nan ga Hashimu tunda bai ɓice ba

Haskenga yana gusuowa
Har ga Abdullah na baiwa
Anyi auren ƴar budurwa
Amina dangin muruwwa
Sai fatauci yarriƙe shi Baba

Nan da ƙare cin amarci
Ya wuce domin fatauci
Sai a dawowa ya tsinci
Hanya ta Madina yacci
Sa'i bai sami zakkuwa ba

Sannu Amina sannu Giwa
Duk ta mataye na baiwa
Wanga aiki kin iyawa
Kin dakon tunjum ga kowa
Ki bushara ƴa ga Wahbi Babba

Tunda taɗɗauke shi ta san
Ba batu ne sam na wasan
Ƴan ƙananan yara kunsan
Bafa kanwa ce ta lasan
Ba macen da ta kai ki ba taɓa ba

Duk wata sai an bushara
Tun na farko har na tarra
Annabawa anka tara
Don tarar Abba ga Zara
Babu al'ajuban da bata  gani ba

Har zuwa ga Rabi na farko
Nan a farko ne na mako
Nanga shashe shabiyun ko
Duniyar nana tayi bako
Wanda ba taɓa jinsa ko gani ba

Tun gabanin wanga hijra
Tun a Taura an bushara
Har a Linjil an kirara
Ahmadun ka faɗa ka ƙara
Har irin siffarsa ba rage ba

Aljanu da su kanyi tsani
Don zuwa sararin samani
Kan su sato ɗan bayani
Sunga sauyi yayi muni
Ba su san manufar Ubangiji ba

Shin azaba ce ta sauka?
Ko ko haske ne ya haska?
Duk kwa sambatu ya ɗauka
Ya zamo tamkar na hauka
Don shirin tarbarsa Ɗan Suwaiba

Ƙoramar nan mai ruwa fal
Ta ƙafe da zuwan na Naufal
Farisa da wutar su mai fal
Ta bice yau ba ta fal- fal
Haske ba za ya bar duhu ba

To gabanin wanga jewa
Anyi kissar nan ta giwa
Sanda arna sunka zowa
Ka'ba  za sui bigewa
Wandaran bai bar su sun hakan ba

Shekarar giwa ta doko
Sammako kai anga iko
Jalla mai damƙa da dako
Haihuwarsa Rabi na farko
Anga haske wanda ba taɓa ba

Shekara ta ɗari biyar ce
Ƙara saba'in kayi dace
Haihuwar Isah fitacce
Ɗa ga Maryamu tsaftatacce
Da ga duk shirkar nasara duba

Can gabanin assubayi
Litinin haske da sanyi
Ya iso sujada yake yi
Kunji mai Sarki Buwayi
Amina bata santa naƙuda ba

Ya shigo dunya a wanke
Harda kwalli harda haske
Ba ƙazanta cibi  yanke
Anyi shayi babu sake
Ɗahirun tsarki gareka babba

Nan da nan aka je bushara
Inda kaka nas ya dara
Nan ga Ka'ba an ishara
Ran Mutsallabi yassarara
Yai tukuici yai rabo da gumba

Take sau kwa gari ya ɗauka
Har kuyangar nan ta Makka
Gun Abu Lahbin ta sheka
Tai bushara nan ya sauka
Ta san ƴancinta ba musu ba

Yai tukuici nan na homa
Harda dabbobi da dama
Dukiya duk sai ya kama
Yin rabo don haihuwar ma
Ɗan uwa nasa wanda bai da rai ba

Sai Mutsallabi yarriƙo shi
Ka'aba ya tawo da shi shi
Yaɗɗaga shi ya ambashi
Jalla shi yabba shi kimshi
Ba'a san sunan a zamuna ba

Yakkira shi Abin Yabawa
Don ya sami yabo ga kowa
Nan ƙasa harma bisawa
Mai riƙon Tutar Yabawa
Ce MUHAMMADU ba da inkiya ba

Duk fasahar larabawa
Duk zalaƙar harda baiwa
Harda hikmar sun gazawa
Inkiyar da ka tanadarwa
Mustapha ba su san ta sun saka ba

Duniya ɗuk ta yi haske
Duk duhu kuma sai ya waske
Don zuwan Manzo na gaske
Shi jakada ne na yanke
Babu limancin da bai riƙe ba

Har a yau fa muna ta murna
Don zuwan rahmar nufina
Harda falalar Jalla guna
Shi ga dukkan alamina
Jinƙai ya zamo ba kui musu ba

Maulidi indai ya kama
Duk masoya sai kwa himma
Ai robon biskit da Lima,
Lukiraka har da  ƙwai ma
Ba irin bidirin da ba mu yi ba

In kana jin kunci zuci
Har da zafi harda daci
In wata na Rabiyyu ya ci
To kwa imaninka binci-
ki fa kar ka barar ba kai awo ba

Dole mui fara'a da murna
Don busharar Dan Amina
Shugaban duk talikina
Da ga Adnan Shugaban na
Dangin mu ku zo mu daina gaba

To wajen yin maulidin nan
Sai a lura da tsarikan nan
Bin shari'a babu cudan-
Yar maza mata wajen nan
Bada yasassun batutuwa ba

Duk darajja har muƙamai
Ya riga ya sami dammai
Tunda shi yazzarce sammai
Ba buƙatar mui ƙirar mai
Ƙarya ɗomin ɗaga shi Babba

Duk halittu ba kamar sa
Mustapha Ango Na Hafsa
Duk muƙamai na wajen sa
Kui bushara masu son sa
Da rabon Firdausi ba ƙasan ba

Sai salati sallamawa
Kan fiyayyen Annabawa
Shugaban kowa da kowa
Mai riƙon Tutar Yabawa
Ran ƙiyama kunji ba musu ba

Godiya ga ubangijna
Wanda shi ne yai nufina
Yaccika min yau batuna
Haihuwar Manzo na Nana
Ba gumin goshi fa ban gaza ba

Ni Bashiru uban Humaida,
Garkuwa, Shu'aba ku shaida
Ni ina son mai Sujuda
Mujtaba ahlinsa harda
Duk sahabbai ban cire guda ba

Nan nake son zan taƙaita
Ba ni son dai tattsawaita
Tun Safar da can nayi ta
Haddatau yaɓɓalgace ta
Sai Rabi' na kuma ta ban gaza ba

Biyu ne dai to a farko
Maulidi farko a mako
Jalla har yabba ni iko
Naggama na saku dako
Allah sa ba don riyar na ke ba

Hijrar ta alif ka sanyo
Kan ɗari huɗu to ƙidanyo
Arba'in sai ukku goyo
Shekarar ce bata ɓoyo
Tarihin bai zamo ɓata ba

Ya zamo miladi dadai
Tara kan Oktoba ne dai
Shekarar alfaini saidai
Ashirin ƙaro da ɗai dai
Haihuwar Isah Nabiyyu babba

Ni Bashar jika ga Binta
Na zamo kwa mawallafinta
Rabbi shi ne yai nufinta
Shi ya sa kaima ka ji ta
Sallama ga Rasulu Ɗan Suwaiba

Godiya gun Jalla Sarki
Wanda yattare shi tsarki
Shi yasa nazzam mawaki
Gun Badaɗina Ma'aiki
Baiwa ce ba da fariya ba

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka