KAINE NA KE SO MUJTABA
Amshi:
"Kaine na ke so Mujtaba
Na san ba zan tozarta ba"
Duk rayuwata kai na ba
Fansa gami da uwa uba
Har dukiyata zan zuba
Domin na ceto Shugaba
Manzon da banga kamarsa ba
Harshen ba zai iya furta ba
Hatta rubutun nan gaba
Bege kawai na saka gaba
Duk lokutana kai na ba
Domin na sami wuƙar gaba
Nan duniya da gidan gaba
Ni kai na ƙe son zan yaba
Ba ayyuka ne nayyi ba
Saidai kawai ƙaunar da ba
Ta misaltuwa ya Shugaba
Shin me ya sa ban gan ka ba
Ga zuciya na fargaba
Sai faɗuwa kullum gaba
Ni banda kowa Jagaba
Sai so wajenka Mujittaba
Ita zuciya na nan gaba
Da dukan fa wanda ta sa gaba
Kai narriƙe gam Shugaba
Na zam maraya ba uba
Na san ba zan tozarta ba
Comments
Post a Comment