MUHAMMADAWA MASOYA ALLAH

MUHAMMADAWA
Muhammadawa masoya Manzo
Allah ƙara kusanci sosai

Basmalah zan faro bege
Rabbana samin kyan hange
Na fito dantse na zage
Baitukan sui tsari jubge
    Agaza Mahaliccin ƙassai
Gaisuwa da salatai jingim
Kan Ma'aikin nan mai tinjim
Kausara ba mai sha lazim
Sai masoyi gun Ɗan Hashim
    Sha'iranga da ba sa yasai

Zanyi waƙen kan ku masoya
Masu begen shauƙin koya
Ayyukan magabatan dunya
Masu begen Ɗan Sa'adiyya
   Na ga har da mutanen Wasai

Jinjina a gareku matasa
Harda manyan ba sa fasa
Baituka gun angon Hafsa
Safiya da dare  ba wasa
   Gun yabon sun dage sosai

Sun fito da muƙaman Manzo
Kariya ma nan sun ƙwazo
Shubbuhohin yaye hazzo
Mu'ujizoji su ma sun zo
    Kan yabo na sa sam ba kasai

Rabbi shi ɗaya zai sakanta
Hiddimar da ku ke wa Binta
Ga mijinta da ma Abbanta
Har sahabbai  ba banbanta
   Duk ciki ba kanwar lasai

Wanda yaiwa Ma'aiki zambo
Ko habaici sai sun ɗebo
Baituka zafafa zubbo
Kariya gun Manzo dubo
   Na ga harda mutan Yakasai

Masu koyin Hassanun nan
Harda Ka'abu da Khansa sannan
Masu bin su a tsari kenan
Busuri da su Alfha ɗinnan
   Har su Rabi'u Ɗan ƴan Ƙosai

Ga nasiha gunku fa zanyo
Shi yabo in dai za kai yo
To ka zam neman ilmi yo
Jahili ba zai yiwu yaiyo
    Baitukan begen sui rassai
Shawara a gereku matasa
Gun yabo kar kuiwo wasa
Nan sani sannan sai ka sa
Wanke niyya kar kai gasa
   Rabbi za ya biya can dausai

Duk abinda ka so zanawa
Nemi malam yai dubawa
In akwai gyara zai sawa
Baitukan ka su zam haskawa
   Don ka tsira ga sharrin harsai

Jinjina ga masoya Manzo
Muhammadawa kunyo ƙwazo
Ko da marka ne sai kun zo
Masu shiɗewa don Manzo
   Allah ƙara kusanci sosai

Rabbi karɓi dukan aikin su
Sha'irai da masoya na su
Sa a mizanin aikin su
Kuskuren su ka shasshafe su
   Faɗiri Mahaliccin ƙassai

Sai salati gun Ɗan Baiwa
Shagaban nan mai yin baiwa
Wanda Allah shi yabbaiwa
Duk mukullan rahmar sawa
   Jannatu lambun mai dausai

Shugabana Ango Hansai
Ni ina ƙaunar nan sosai
Ga shi ba ni da tsanin nan sai
Nan gare ku nake so in sai
   Inda kai wahala an fissai

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka