Na Gwanaye

NAGWANAYE

Jinjina gun Gwani Wali na Ilahi
Nagwanaye mu gaida Abdullahi

Dan Aliyu uban Aliyyu Kisa'u
Shi da Asim da ma Gwana Zahra'u

Zan yabo ne ga haziki na tilawa
Duk ku huta ku zo ku daina adawa

Shi ya zamto ina kira kahuhu
Ai Gwani ne mu gaida shi Na Ilahu

Shekaru shidda sun riga sun fece
Dalibai har rabin dari suka dace

Sunyi saukar da ba'a ce ta dabino
Sai ku kauce fa mahiran sun danno

Rabbana shi kadai kawai zai saka
Wanga aiki na juriyar nan taka

Don Gwani yayi hankuri kan yara
Har ya zamto fa dalibai  ya tara

Ba shi kaushin hali da zai kore  su
Sai kwa jinkai da tausayi domin su

Dalibi gun Gwani Kabir Ya'kubu
Ga Gwani mai yawan kwami ba aibu

Har ijazah mutum biyar aka baiwa
Ba dukan dalibanga ne su ka kaiwa

Darajar ta ku gane mai girma ce
Ba'a samun ta sai kwa an tantnace

Sannu gwarzo da kwaikwayon Minshawi
Da  Huzaifi kamar na ce masa rawi

Ni ina sonka ya Gwani Abdullah
Don tilawarka sai kwa masha'Allah

Don qira'a bakwai ka zo kai darasu
Shi fa gadon gidan su ne ma Warsu

Na yi fatan Wahab ya bani ya taku
Ko rabin ta ku don kwa ba na shakku

Duk watan azzumi idan ya kama
Ba bu hutu gare shi domin hidma

Zai qiyamu ya dangaana tafsiri
Sai da hantsi ya kara yi yai Kari

In kwa goman tahajjudi ta kama
Babu hutu gare shi na duka ma

Rabbana dai ya sa bisa mizani
Ga waliyyin mu Khadimul Qur'ani

Gangaran ne ku bada fili yara
Gun tilawa idan Gwani ya fara

Sallamata wajen Uban Zahra'u
Har sahabbai, da tabi'ai qurra'u

4/3/1443 AH
11/10/2021

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka