SANYIN IDANIYA

SANYIN IDANIYA

Ganin Sidi shi zai bani sanyin idaniya
Mafarkinka shi ne nawa buri a duniya

A duk randa nassan wanga sa'a da safiya
Fa zan fara albishiri da murna da dariya

Idan na mace ranar fa Sam ba hayaniya
Gama an cikan burin da ke rai guda daya

Aya Sidi mai sona ina kara godiya
Bisa son da kai min wanda ka zarce ma iya

A sallah ka ke samun sa sanyin idaniya
A begenka ni zan sami nawa gaba daya

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka