SUBHANAKA ALLAH

SUBHANAKA ALLAH WITIRI

Subhanaka Allah Wittiri
Absa sabonsu mutan gari
Fa bara'a ta ce zahiri
Karbeta ka yi mini hanzari
Kan aikin wawayen biri

Allah shi yayyi samaniya
Da kasa da dukan na tsakaniya
Ba abinda ya ke da kamanniya
Da Ilahu makagin duniya
Mai ji da gani ne Zahiri

Allah daya ne duk mun sani
Shi ne kudurin duk mumini
Duk wanda ya ke daukar wani
Matsayin Allahu Muhaimini
To ya bata hanyar Fadiri

Yan hakika masu fagabniya
Wai komai Allah don tsiya
Ku sani hanyar durkaniya
Ku ka kama ga hauragiya
Qul huwallah Allah Wittiri

Subhanaka Allah Mai Sama
Sabon da su ke ya girmama
Ma su karyar bi gun Barhama
In sun ki su daina sun sama
Tsine musu Allah Qadiri

Dukkan taklifi kun ki yi
Wai kunyi fana'i ba ku yi
Sallah da ibadar Muhyi
Kun kauce dukkan wahhayi
Addinin bogi ku ce giri

Har zagin Allah ma su ke
Bin mata har da giya su ke
Sha ba kunya don sun sake
Fa akidar sai yado take
Rusa Gwani don zikkiri

Subhanaka Rabbul Izzati
Amma yasifoona bi siffati
Ya halicci mutum har jinnati
Sannan ya tanaji jannati
Don mai tauhidin Qadiri

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka