TARBAR WATAN MAULIDI 1443H

 Tarbar Watan Maulidi 1443H


Ya Rabbana ka kai ni nan da maulidi

Domin na wasa Shugaban mu Ahmadi


Na yo salati gunsa babu adadi

Na je wajen tarurruka na maulidi


Na yo yabo na harraka har da kidi

Na watsa kyautukan turare da kudi


Da tamburan yabo ga Sidi Ahmadi

A bamu siratun-nabi Muhammadi


Na kara sonsa koda yaushe da dadi

Na dinga ba shi kariya gaba-gadi


 Na samu walwala a rai ba adadi

Na samu sirrukan yabo da madadi


Na sake baitukan yabon kamar badi

Na yo hawan sarakuna har da nadi


Na sanya tagguwar kawar manyan kudi

Ranar zuwansa Mustapha na ke fadi


Ya Rabbana Raya ni nan da maulidi

Don nai farin cikin zuwan Muhammadi



Na Annabi Sanda

24/3/1443

2/10/2021






Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka