TSABGAR HAƘIƘA
TSABGAR HAKIKA
Tsabga na dauka nai nufin zan tafka
Kan ja'irannan masu yinta hakika
Zan doki kan duk mai uba har shege
Bauta ga Allah in yanai da hadaka
Subhana Allah bai kini ko dangi
Sarki Gwani wannan da ba shi da tamka
Allahu dai ne ba batun yin shirka
Tilo, guda, qwal kansa ba ma shakka
Alfardu ya aiko da duk manzanni
Da riko ga rauhidi a bar wata harka
Kakan mu Nuhu da yai ta faman da'awa
Kan masu bautar Wadda harda Ya'uƙa
Yai shekara curin dubu ba hamsin
Yana ta fama don su bar yin shirka
Ita kaddara kullum ta na kan fata
Ambaliyar Ɗufana duk ta halakka
Allahu ya aiko dukan yan sako
Da nufin a bauta mas a daina hadaka
Wai yau a al'ummar Masoyi Mujtaba
An samu shaidanun da sun fita zakka
Guzma da sunka fake da harbin karsana
Sun maida komai rabbu wai la shakka
Sun maida zagin Jalla ma wata sara
Lokon Afawa Mustapha su ka taka
Sun haukace tuburan a wanga akida
Don yayi nisa mai kira bai jin ka
An ba su wurdin bogi wai na wusuli
Sun hargitse karya dakon ta su dauka
Sun tara suma tum kamar Bammali
Sun ratayo carbi hadi ga sarka
Har gobe na rasa me su ke jan lazumi
Tundai da ka ce wai ana bautarka
Ka daima sallah ka rike masha'a
Kai dan hakika dole in zargeka
In an kira Manzon mu ba sa shauki
Sai an kira Botoromi mai shirka
Sun ce Buraima fa wai yake ta halitta
Sun kama ganye gimshiki sun sauka
A cikin halittu babu dai ya Rasulu
BawanSa ne ManzonSa ne Mai Makka
In kai ibada ba ka kai Jibrilu
Har gobe bawa ne a gun Mai Dukka
Inyasi Ibron Kaulahar fa ku gane
Bawa ya ke shi ma ku bar yin shakka
Sunce ku boye kar ku bar mahjubai
Su fa san akidun nan da ke a hakika
To in shari'a ce meye zan boye
A cikin nadin nan kwai kaya mai suka
Allahu Allah dai guda ban shirka
ZatinKa, siffofi da ma sunanKa
Subhana Allah ayyukan wawaye
Kada kassaka har ni idan kai damka
In zaka roka to ka dau kokonka
Gun Rabbana kofarsa jeka abinka
In taimako ne shi kadai zai yi ma
Gunkin na Shehi fa ba ya anfanarka
In ka saka a abin hawanka da neman
Ya tsareka to ka sani fa dai kai hauka
Ya za'a ce hoto na waccan mushen
Zai kare sharri ko ya anfaneka?
Mun gode Allah tunda ya shirye mu
Ba don dabara sai da shiryarwarKa
Allah ka karbi batunga kan uzirina
In kayi narko fidda ni a fushinka
Subhana Allah tsarkaka duk taka
Girma buwaya du su na hannunKa
Allah ka sa tuta ta tauhidinKa
Tai filfili duk ko ina kan shirka
Ni ne Na-Manzo mai yawan kaunarka
BawanKa mai kyamar ayi maka shirka
Nayi ta ne a Safar a farkon mako
Na alif dari hudu arba'in uku maka
Comments
Post a Comment