ALLAH JIKAN MALAMI MAI QALA HADDASANA
Allah jikan malami mai qala haddasana
Sannan ka sa shi makotar Sayyidul Kauni
Ya sha wuya gori ka hada batun asali
A hakan ya sauke littafai harma Sahihaini
Farkon fadan sa da yan ilimin Hakika ne
Su ka zam kiransa da Ahmaq zantukan muni
An fara dagar da tsagin Qadirawa ne
Magana ta Sawi da yai gefen Jalalaini
Aka ce a maida shi Ghana wai na haure ne
Kuma wai aqidun sa sun sabawa Qur'ani
Duk wata kutungwuilar da sun kai ta zamo banza
Domin ya na nan da tanyon Jalla Ramhmani
Ya rayu kam kuma yai tsufansa mai kyawu
Kan burtalin sunna hakaza na Qur'ani
Yayinda Bawa na Inyas yayyi banbarma
Malam ya fede Hakika tunda tai muni
Su ka je wajen wani wai shi Tambari Yabo
Ba sa batun kare Manzo Sayyidul kauni
Ya fara da'awar nan tun a Bayero ne
Darul Hadisi ya koma don matsin tsanani
Alhamdulillahi Malam na yi ma barka
Da ka furfure kan hadisan da ga Adnani
Ya tarbiyar, ya zaburar sannan kwa ya koyar
Fanni na ilimin hadisi har da Qur'ani
Baiti na Larabci da kullum shi ya ke ta fada
Zan fassara ko zan iya to zo ka dan jini
"Duk wani sani in banda Qur'an na wofi ne
Sai kuma hadis hakaza sanin dini
Ilimi fa sai ya zamo kwai qala haddasana
Abinda ba shi ba rudi ne na shaidani"
Allahu Akbaru ga zance na mai hikima
Da Malamin mu ya ke zance ya na nuni
Ranar Ahad yai batun shi kam fa zai huta
Yai dariya yai sallama sam babu alhini
Ashe ashe hutu na Karshe shi ya ke dauka
Ba wanda yassan nufi nai ko ya yo auni
Yau Juma'a na ji ne can inda BBC
Malam fa ya tafi can izuwa ga Rahmani
Ranar hudu ga Jumada wadda ke sani
An tashi kai nai fa kowa na ta alhini
Hijira ta forteen ka karo arba'in da uku
Bakwai Janairu twenty-two a Rumani
Allah jikan Malami mai qala haddasana
Duk ayyukan sa na khairi sa a mizani
Sannan ya tashi a gefen wanda ke shauki
Manzo nufi na a gefen nasa Al-Ghani
Nai sallama da salatin wanda an baiwa
Qur'an da hikma ta sunna don ya yo nuni
Ni ne Na'Annabi mai begen masoyin ku
Allah jikan Amadun Bamba fa Al-Ghani
Comments
Post a Comment