ALLAHU RABA MU DA SAKARCI

Mabiya Blacky Bakin Bawa
Ku tuba ku daina munafurci!

Bismillah Allah zan fara
Kasidata kan yan Faira
Ina so ne dai sui lura
Su tsira su bar duk shashanci

Dubun tsira a wajen Nura
Ma'aikin nan Abban Zahra
Muhammadu wanda ya je Isra
Da alaye har nas da aminci

Ina ta kira gun yan Faira
Ku bar bautar gunkin Ibra
Ku kama Tabaraka don tsira
Ku daina Hakikar sakarci

Ku san Allah ne mai tsara
Dukan lamari in ya jera
Baya gajiya ko yayi jira
Jiran Ibron yai sassauci

Dukan Kassai shi yajjera
Hakan sammai kuma ya dora
Fa ba shi jiran wani yai gyara
Tabaraka Allah Mahalicci

Ina kuke ya ku yan Faira
A sanda akai sama an jera
Ina Ibron ya ke ga fa dara
Ku ban amsa ba son zuci

Kuna cewa wancan Ibra
Halittu shi wai yattsara
Mutum ya ke ko ba ku dibara
Allahu raba mu da sakarci

Idan Allahu kwa ya tsara
Nufin shiriya sai yaggyara
Idan kwa bata ya zamo qadara
Fa za ku zamo a munafurci

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka