GURBIN IDO

Gurbin ido ba zai zamo ba idaniya
Sai mui kwatance don rabauta bai daya

Wane mutum inji muttuwa da ake fada
Turkashi na san za ku gane gaskiya

In ka ga linzami ga Doki ne kawai
Wane su kaza kun sani ta Sha wuya

Wai ni ake cewa in zo in dafa kai
Inji Kantamawi kunji wai don zolaya

Ya bani kunyar sai da ma nattsorata
Tuba na ke yi Kantamawi gaskiya

In banda zuhdu na gingimemen malami
Da tawali'un manyan da ke kin duniya

Ya ni da dan titibiri mara ganiya
Zan kai kamar Garban mu Sarkin Kafiya?

Fata na san danshin ku  ko nai azzama
Zan zo a shafan kai su bar min dariya

Allah ya ba mu ya ta ku ko can lahira
Na san ku na kauna ga Khairul Anbiya

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

Ya Rabbana raya mana Muhammada

MU TSARKAKE ALLAH