GWANIN MAI KOYO
Bismillahi za na tsaro waƙa
Ta gwanaye ciki da 'Musan Gayya'
Yau ina alfahar da 'Musan Malam'
Ya zamanto gwani abin a kiyaya
Da ace babu masu koyo tabbas
Da gwani ya zamo abin jin kunya
Tun ya na ƙanƙani mu ke tatata
Ga kafafun sa sunyi ƙwari gaya
Na yi murna da ɗalibin yaffini
Ni kawai sai na ce da shi Ala raya
Ga fa Musa Rufa'i mai albarka
Haziƙin ɗalibi maso jin kunya
Ya kasance tsatson 'Karin Kundi' ne
Ga shi ɗa gun Rufa'i mai tarbiyya
In ka koma ta ɓangaren Barnoma
To gwanintar jinin su ne zurriyya
Rabbana sa ya zam na tsoron na ka
Kar ya zamto dugadugan sa su juya
Tsarkake zuciyar ka sa ikhlasi
Gun tilawa ka sa ya zam ba shi riya
Rabbana ƙara ba shi ƙarfin hadda
Don ya zamto gwanin da ba bu hamayya
Godiya gun Rufa'i jikan Hamza
Muqri'i ne a daina ma jayayya
Bai da aikin da yawwuce Qur'ani
Sa ya cece shi ran da duk za'a tsaya
Ba tijarar da taffi yin Qur'ani
Don kwa 'Ahlin Ilahu' ne nan dunya
Daga Anasun idan ka dau Dabara ni
Za ka gane batunga ba jayayya
Ba asara cikin ta sai dai riba
Da tukuici mafi yawan sakayya
Gun su Allah ya bar tsaron Qur'ani
Da tsarewar Sa sun zamo makiyaya
Rabbi ladan ka kai shi har ga uban mu
Marigayi Uba Gabari Na Yahya
Ya kasance mutum maso Qur'ani
Ga tukuicin Kareemu nan tun dunya
Malamin ya zubo wasiyya goma
Da ga shehin sa ne Ridha mai aniya
Fari ya zazzago dukan isnadi
Har Ma'aiki ya dangana ba tawaya
Ya kwa godewa Rabbana da iyaye
Malamai har da yan uwan zurriyya
Za na kwan yau farin ciki da nishadi
Dalibina cikin sahun yan manya
Nan na ke kare baitukan taya murna
Gunsa Musa da sha-bakwan jeranya
Da ace babu masu koyo tabbas
Da gwanayenga za su zam jin kunya
Yau Jumada Na Sani ya kai shidda
A alif sai ɗari huɗu ka ƙidanya
Arbain sai ukun da za kai ƙari
A ƙidayar mu ai nufi Hijriyya
Lahadin ce tara wata na Janairu
A dubu biw twenty-two Girigiyya
Ni Bashiru Uban Humaidah Na tsara
Ala sa nai ta ne da kyawun niyya
Hamdala gun Gwani, Hakeem Rahmani
Sai salati akan Uba ga Ruƙayya
Comments
Post a Comment