KANWAR LASA

KANWAR LASA

Fa Walidan Manzon mu gagara gasa
Ina yabon kanwar da ta wuce lasa

Bismillah Allah ni na ke farawa
Sarkin da shi ne dai na ke bautawa
Baya azaba tun gaban aikawa
Zan yo yabon Abdullah harma Giwa
Fa Walidan Manzon mu Angon Hafsa

Cecekucen ne ya ki yai karewa
Wai duk akan Abbansa har Yar Baiwa
Fa Amina  yar Wahbi kin wuce kowa
A duk matakai kunga  sun tserewa
Mai son ku shi ne yau na ke rarrasa

Maganganu ba kan gado mun ji su
A bayyane tun da ana  boye su
Akan makomar wai Iyayen Shamsu
Wannan da shi ne yazzamo dawisu
Ga duk ma'aika kunji dan Abbasa

Yau na gaji shi ne na ke yin raddi
Ga masu zance ba bu kai ba gindi
Su na ta sukuwa sun hawa ba sirdi
Ana ta zance kan Iyayen Hadi
Wannan abin ya sa jini ya tafasa

Ka na da riba in ya zamto ka ce
Wannan karatun nan kamar ka zauce
Kana fada harma kana wani huce
A ranka gaba ko kiyayya dai ce?
Ga Mujtaba Manzon mu raina fansa

Wannan ya sa ma Audu yai tawaye
Ya ce hadisan duk akwai jurwaye
Ya zana daga har yace ya janye
Akan mutuncin Mustapha ya waye
To yau karatun ga shi har an nisa

Idan ana wannan karatun ni kam
Duk zuciyata sai na ke Jin ta zam
Ta na ta kunci ga shi ta daure tam
Ban kara yarda ni da wannan sam-sam
Don walidan Manzon mu sun wuce wasa

Idan na ce kakan ka Dan Jalingo
Arne ya ke tsauni ya kan dan hango
Leken gari da ga tsaunukan Jalingo
Yanzun ya na Sijjeen ana jijjibgo
Shin zai zamo laifi? ka zo ban amsa

Kai ka sani ni na sani kam kado
A can tsatsonka sunyi bautar dodo
Rawa da juyi har su na yin dodo
A tsaunukan bori su kan tattado
Me yahhana shi kayyi littafansa

Dukkan iyayen Mujtaba manya ne
Zabi na Allah ne a dukka mutane
Ya dinga tata kana sai ya tsine
Dukkan su sai dai wane ko ko wane
Sannan ta aure ba batu yasassa

Sannan ta yaya za'a Kona mutanen
Da su ka zamto babu sako sannan
Kafin a aiko sun riga  sun bar nan
Su ne iyayen nan a gun Dan Adnan
Allah Karimi ne mu bar yin wasa

Tun Adamu kai dangana kan Abdu
Yana ta linkaya cikin sajjadu
Duk muminai ne kan kadaitar Ahadu
Allahu kenan Wahidun Assamadu
To duk ciki sam ba bu kamwar lasa

Ko Azaru ai Dan uwan baba ne
A wajen Badadin ya kamata ku gane
Tarikhu ne tsoron sa tarihi ne
Ka je ka duba tunda kai 'malam' ne
Kawo hadisan naka ai ma darusa

Kawo dalilan naka kai sususu
Na yo shiri sosai na rurrusa su
Idon sa kyarr kun ganshi nan dan kusu
Dan kwangila ne dan ya tara asusu
Allah wadan mai guntsi sai yaffesa

Sai ka fada don ka gani littafi
Ka dinga zancen mai kwakwalwar kifi
Batunga ya sa duniya tai zafi
Ga duk masoya Annabin mu Nazifi
Jalingo ka cuce mu Allah ya isa

Ba zani yafe kana ba zan mance
Wannan fushi kam babu ranar wuce
Ka sa mu kunci kan bari gun zance
Na rassa ma wallahi ni me zance
Ko me nace mas wallah bai kai fansa

Indai sani na za ya sa  tozarta
Ga Mustapha wallahi ban so kwata
Amina-Abdullahi sun gawurta
Su ne mahaifan Shugaba na Halitta
Ko nan ka san kanwar su ta wuce lasa!

Tsira amminci nan ga Manzo Mahi
Da Amina sannan da Abdullahi
Ai Walidan Manzo abokin Ruhi
Jibrilu sarkin ma su bin Lillahi
Na gode Allah Rabbi ni bawan Sa

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka