MAJE MUSTAWA

Rabbu shi ne gaba
Inna sanyo gaba
Zanyi aikin da ba
Mai zaman jagaba

Sallama sarmada
Kan Habib Ahmada
Alu sahbu kada
Ban cire wane ba

Kan batun Issira
Har gaban Mi'iira
Nan ga Tahtas-Sara
Ya wuce can gaba

Ai Jubo ne ya zo
Nan Buraƙa ku zo
Zan batun ba hazo
To ku bar fargaba

Nan da nan sai Ƙudus
Sai ka ce dunduɓus
Ya yi sallah Ƙudus
Shi da duk Ƴan Gaba

Sai ya miƙa sama
Sunyi duk sallama
Sai ayo tuhhuma
Kan a buɗe gaba

Ya ƙure har bakwai
Ya ga manyan da kwai
Anbiya ba bu wai
Ya shige har gaba

Takkanas yattafi
Inda ba ko rufi
Ba ciki ba kifi
Ba kwatancen sa ba

An wuce duk sama
Har magaryar ga ma
Wadda ke ƙurya ma
Hauni daman ka ba

Ba yini ba duhu
Ba bu zafi lahu
Har da huffin sahu
Bai cire na sa ba

Ya maje Musatawa
Can gaban nan kuwa
Har magaryar zuwa
Ban ga tamkar ka ba

An yi kimshe garai
Gaisuwar nan warai
Can a Tahiya sarai
Je karanta gaba

Sunyi gani da shi
Ga-da-ga shi da shi
Tarjaman babu shi
Shi kaɗai Mujtaba

Ya yi wahyin abin
Nan da yabba Mubin
Shugaban masu bin
Jalla ba ƙahru ba

Tas ido nai na ka
Mustapha mai Maka
Yaggano Mai Duka
Ba musu Jagaba

Ba batun shamaki
Nan gaban Ƙhaliki
Kai daki kan daki
Sirru ba jahru ba

Wassu ya bayyana
Ka na ya adana
Wanda yazzana
Gun masoyan gaba

Ya ga ɗakin sama
Wanda ke yin kama
Nan da Ka'aba gama
Ba su saɓon sa ba

Su ibada su ke
Nan ga shi sun fake
Sai ɗawafi su ke
Ba'a maiman su ba

Anka karɓo biyar-
-Goma sai an mayar
Kunga sallah biyar
Ajru bai sauyu ba

Sanda Manzo ya zo
Makka an dandazo
Don ƙurewa ku zo
Rabbu bai bar su ba

Sunka zam tambayar
Nan ta ƙwaƙwa su yar
Dole sai sun mayar
Zantukan Shugaba

An ka ɗau magiji
Duk na hanyar ku ji
Kuskure an guji
Don kwa bai yi shi ba

Har irin ayari
Ya faɗa Munziri
Sanda an jinkiri
Shamsu bata faɗi ba

Sunka je gun Bukar
Wai abokinka har
Can Ƙudus ya isar
Duk dare kai haba?

Sai Bukar yaffaɗa
In Ma'aiki daɗa
Tabbacin ya faɗa
Ba musu zan yi ba

Kunji Siddiƙu ne
Sahibin Ɗaha ne
Sallamawar sa ne
Banga tamkar sa ba

Kafirai sun turus
Kana sun funfurus
Bakunan sun murus
Gasgatar Shugaba

Khaliƙin duniya
Rabbana godiya
Sai salati ga ya
Khatamul Anbiya

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

Ya Rabbana raya mana Muhammada

MU TSARKAKE ALLAH