DUBORA INA UMMU.QABEEH?
Banga ribar ja'irai ba
Masu zagin Shugaba ba
Ɗaukaka girma da haiba
Rabbana Mahmudu yabba
Masu ƙinsa a hir ku daina gaba
Inko kunƙi ku daina walla
Za ku saura ku na ta ƙwalla
Har fushi ya kashe ku zalla
Mujtaba zaɓi na Jalla
Mai ƙinsa ba zai ga fa'ida ba
Da a Denmak ko Faransa
Ne mu ke jin masu ƙinsa
Na ta barkwanci da wasa
Wanda ke taɓa janibin sa
Ba mu yarda da wagga shaiɗana ba
Ga Yahudu haɗa Nasara
Harda arne mai tsirara
Bai da aiki sai harara
Martabar Manzon mu Nura
Yin hakan bai tauye martabar ba
Babu alfahri batun nan
Shugaba ne gun mutanan
Can na farko har zuwa nan
Ƙin ku koko son batun nan
Haka dai yake bada gardama ba
Arniya a garin na Shehu
Ta yi ɓanɓarma da ihu
Kan Fiyayyen nan Fasihu
An baje ta su na ihu
Ba mu san manufarsu duniya ba
In tace Isah Na kowa
Wai Ɗayan Uku ne da sowa
Har ta nemo amsa kuwwa
MA BIHI KAFARAT ta zowa
Ba ruwan mu ba za mu kai ido ba
Wanda yattaɓa Shugaban mu
Ba mu ji kuma ba gani mu
Kansa duk mun bada ran mu
Don mu fanso Shugaban mu
Ban ji mai zaginsa ya haye ba
Munji Alƙali Iyalu
Ya faɗa kuma ga dalilu
Wanda yattaɓa Ɗan Halilu
Sai kisa ba sauya ƙaulu
Tuba bai sauya yin hakan ba
Sai a bar shi a gun hakuma
Don gudun tashin husuma
Bincike ita za ta soma
Kar ya zam an bada dama
Ai hukunci ba da tabbaci ba
Koda dai na san mutane
Nada shakku kan abunne
Kan batunga na Abdu Wane
Wanda yai zagi Kano ne
Shi ya sa ba su bar ta ta ware ba
Kai ko mai sukan hukunci
Ai kisan duk wanda yacci
Duk mutuncin Mai Aminci
Don ka burge ko tukuici
To ka tuba ka zam biɗa ga Rabba
Rabbana tuba mu ke yi
Kan abinda wasun mu ke yi
Keta alfarmar Nabiyyi
In azaba za ka zam yi
Ka tsare mu fushinka don na Garba
Kai salati har salami
Ƙan sa Manzon nan Imami
Shugaba Badarut-tamami
Kunji mai yaye gumumi
Sarmadan ƙaunar sa ban tsaya ba
Comments
Post a Comment