ƘAMSHIN MAJE ARSHI
Abban Kulsumu Maje Arshi
Bismillah da sunan Zul-Arshi
Rahmanu Majiƙan bayin shi
Harshe na sanya yai laushi
Zan begen Mai kyawun gashi
Tsira da aminci a gare shi
Baban Zahra'u da Ibrashi
Ahli har duk a sahabban shi
Haka nan duk mai bin sahun shi
A cikin wannan na ɗau ƙusa
Zan ƙero sirrin kamshin sa
Da gumi nasa wanda ya ke fesa
Madarar kamshi na buwayar shi
Fa Anas Ɗan Maliku ya furta
Yanayin ƙamshin Babban Binta
Da ga nesa da zarar ya gifta
Fa ake gane dosowar shi
Ga Ummu Sulaimin innar sa
In ta so miski mai ƙamsa
Gashi da gumin sa ta ke kwasa
Domin haɗa kamshi mai tashi
Mata a Madina su kan samo
Mazubi domin in ya zarmo
Su tara su aje domin kamo
Baki na zare da turaren shi
Yara su ka tura don neman
Shashi na gumin Manzo Mamman
Da kwalabe ne ma na musamman
Don kowa ya san ƙamshin shi
Da Anas Ɗan Maliku zai ƙaura
Ya bada wasiyya da ishara
In likkafanin sa kwa an gyara
A haɗa da gumin sa maje Arshi
In an hada miski da gumin sa
Lallai kamshin nan zai nisa
Sannan dunya ba bu irin sa
Don sirrin mai hasken goshi
Tsira da aminci.a gare shi
Abban Kulsumu Maje Arshi
Comments
Post a Comment