BONE KAN KU
A kan gauƙan da kun kai kui hawawe
Ace Manzon da babu kamar s akwata
Ku ke wa ba'a fa kun san kunyi wauta
Ina zatgin ku zargin bai zaya ba
Ina zagin ku zambo ban raga ba
Akan ƴanci na furci sun ka yo wai
Da farko har da arnan sun ji bawai
Ama manyan musulmiya kona oho
Fa sai ƴan kasuwa ne sun ka eho
Suna Allah wadai kan wanga assha
Musulmai hankali duk ya yi tsahi
Ina.wai duk ƙasashen masu fetur
Musulmin nan cikin su su dinga tur-tur
Fa fetur na mu ba shi zuwa ga Denmak
Ku bar Dolar ku, Sefa koko Dochmak
Kaza dukkan ƙasashen nan na yamma
Akan cutar mu kullum su ka yimma
Fa ranar duk musulmi sun yi shewa
Gama kalmar Ta'ala tai ɗagawa
Daɗewa Ali Mazrui ya yi sharyi
Akan shi feturi Allah Buwayi,
Ya na jibge shi ne gun duk ƙasashan
Musulmai koko inda su kai yawa shan
Makammin nan da Allah yaffa ba mu
A ya zarce su nukiliya a gun mu
Musulmi na kiran duk masu ilmi
Na sadarwa ku tashi ku dinga ƙaimi
Akan radɗi ga arna masu bante
Su na yawo kanar talbal-batete
Idan sunce kule sai kui ta cas cas!
Cikim hikima da wa'azi cancaras cas
Tsiraru ne fa sai zaƙi na.baki
Muƙunshin gisshiri kam ya fi zafi
Musulmi gun yawa in su dubu ne
Dubu biyu za su kora ko da ja ne!
A yau mun zan fa taron tsintsiya ne
Da ba shara a hir to za.mu ƙone
Ina ta kiran musulmi ƴan uwana
Mu tashi mu bar kasala har da kwana
A yau tsari na jari ne fa hujja
Mu ce a'a ga dukkan tasu haja
Da hudawa jini ne anka tadda
Da son afwa fa sun aiko takarda
Ama laifin da sun kai ya ƙazanta
Fa ba afwa a sannan ba nu manta
Ilahi Annabin ka ka yo wa hakka
Fa ɗaman alƙawar kai tun a Makka
Na kare izgilancin masu shirka
Akan Manzo Muhammad Annabin ka
Ta'ala ga su nan kuna kana ga ka
Kayo damƙa irin wannan fa taka
Da ƙarfi gun ka na san babu shakka
Fa kafircin su sam bai gagarar ka
Daɗo tsira darajja har karmci
Bisa Manzon ka Ahmadu har aminci
Ka yi musu yanda kai wa kafirawa
Na farko inda ƙari kai daɗawa
Kamar Ɗufana kan jama'a ta Nuhu
Da iska kan Samudu su dinga ihu
Da tsawar nan guda ɗai kan Samudu
Da kantafin kifarwar Alu Luɗu
Ka mai da saman su shi ne ƙarƙashin su
Ka bi du da damima ta ruwan duwatsu
Ka yi musu yanda kaiwa mutan Shu'aibu
Da ke tauye shi mudu sun yi aibu
Ka kai su tsakan ruwa sannan ka shafe
Kamar Fir'auna masu riƙon madafe
Ka aiko dandazon tsuntsu-duwatsu
Kamar mahayan na giwa sui kisan su
Ka aiko dukkanin narkom azaba
Haɗo har wadda ni ma ban sani ba
Gama ka shafe arnakun gaban su
A ƙarfi har da ƴaƴa dukiyar su
Kaza tarin gidaje har sanin su
Ama yau sai kawai tatsuniyar su
Haɗa har duk ƙasa mai goya baya
Da wanda akan batun ma ke ta kunya
Haɗe har majlisan nan ma ta Niwyo
Game har karnukan su walau a Auyo
Ka aika ruwa tsunami ya dinga bori
Amam dutse da zalzal masu tsauri
Ka sa yunwa, fari duk lardunan su
Kaza yaƙinda cuta addabar su
Musulmi na yi jaje duk a gun ku
Makoki ne muke kam babu shakku
Mu dage addu'a ita ce makami
Mu ɗau keyboard da raddin nan na ilmi
Ayo raddi duhun nan duk mu yaye
Gama dunyar a yau ta zam ya ƙauye
Akan wannan fa rana za ta kisfe
Ya zamto wanga haske ya fa shafe
A ran ashirin tara ga wata na Marshi
Ya maimaito azabar nan ta lumshi
Kusufi anka yo don razanarwa
Da cewa Jalla shi sam bai macewa
Mu san girman sa Manzo ya fi komai
Cikin ƙassai haɗa duk har da sammai
Salati kan sa mai kamshi da.haske
Da duk wani mumini mai ba shi sulke
B.I Unar
13/Muharram/1427
11/2/2006
Digitalized on: 12/9/2023
Comments
Post a Comment