MIFTAHU MABUƊIN ALJANNA

Miftahu Mabuɗin Aljanna

Don shi zai buɗe Rilwana


Bismillah da sunan Subhana

Mai Jinƙai shi ne Rahmana

Tsira da aminci su gudana

Ga Rasulu fiyayyen man kana


Waƙe ne hallau zan tsara

Kan keɓantar Abban zahra

Bayan dunya daɗa an ɗora

A ƙiyama can ma zai nuna


Tuta ta Yabo na hannunsa

Babban ceto na daman sa

Allah sai ya cika zancen Sa

Zai bashi ya bashi da zai murna


Bayan turkaturkar ceto

Al-Muntaqimu ya fuskanto

An je gun kowa sai kaito

Gwarzon ya cane ku tawo guna


Ni ne da ita a bisa tsari

Yau Allah ya cika alƙawari

Zan cece halittu gun hatsari

Sai yai ta kirarin Subhana


Rannan zai faɗi ya na sujada

Da kirarin kimshe daga Ahada

Allahu ya ce ma sa Mahmuda

Yau babu ibada ba sauna


"Roƙe ni na baka buƙatun ka

Kuma cece na bar ma ceton ka

Yau ranar nunin girman ka

Ga halitu" zancen Subhana


Bayan an jingina mizani

Allahu Tabaraka Rahmani

Ya ware na dama da ƴan hauni

Ƴan dama su doso aljanna


Nan ne za ai cirko-cirko

Sai ga Manzo ya durkako

To kun ji fa wanda ake dako

Nan zai nuna shi na daban na


Ya ƙwanƙwasa ƙofa an amsa

Waye a tanan? Zancen na sa

Zai ambaci sunan nan nasa

Gaba za ku ji ɗokin Rilwana


"Domin ka kawai zan buɗe ta

Domin haka nan aka umarta

Nai dako tun ga halitta ta

Yau ni ma ga shi ina murna


Daman kai ne fa mabuɗinta

Tun ran da Ta'ala ya tsireta

Mai Alfarma Baban Binta

Taslimi da yabo zai nuna


Sai kai ta bushara mai son sa

Ceto dai tabbas na gun sa

Mai so zai riski mosoyin sa

Tabbas wannan alƙawari na


Allahu ka ƙaro taslimi

Ga Abul-Ƙasim sarkin Ilmi

Ya ce mana in mun taslimi

Ɗaya Allah goma fa zai zana


Miftahu Mabuɗin Aljanna

Don shi zai buɗe Rilwana





Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka