MUHAMMADU YA FI KOWA
A yau kuma zan Safa ne har da Marwa
Akan duk masu karyar wallafawa
Taqiyyar son fiyayyen Annabawa
Da bai iya son sa har ya ji ya fi kowa
Akwai wasu sun amai sai sunka lashe
Mu na nan har jinin mu diga ta ƙarshe
A tsarin kare Manzo Ɗan Abashe
Da cewa duk halittu ya fi kowa
Idan kai ba ka yi to ba mu fili
Batu kan martabar jikan Khalili
Muhammadu Mujtaba Yayan Aqili
Mu na kai har mu koma can kushewa
Faɗan nan ba na mai tsoro ba ne ba
Idan za kai ka jure duk azaba
Anan dunya a can ko duk da riba
Fa sai dai ɗan kucaki bai iyawa
Idan na tuno guruf ɗin ƴan hakika
A shafin Facebook don yaɗa shirka
Da daukaka shehinai kan Masu Makka
Takaici har hawaye nai zubarwa
Idan kun tsuke baki ni ku ji ni
Ba zanyi shiru ba ko zan karɓi tsini
Takobi, tsitaka mashi biyo ni
A tsagin kare Manzo ban gazawa
Idan ka ji wanga waƙe kaffusata
Munafunci da tsatsa sun yi kanta
A ƙoƙon zuciyar ka idan na keta
A ƙaunar Mustapha ban ratsa kowa
Idan ka ji ka fi son wani kan Muhamman
Ka san cewa da saura gun ka malam
Hadisin Faruku duba musamman
Wajen AL-ANA kai kaiwa da jewa
Idan wani ya faɗi to za ni ƙara
Na ƙara fade a waƙe ma na rera
Ma'aikina da shi ne zan gadara
Ta cewa duk halittu ya fi kowa
Idan haka ba shi yi ma sai ka doɗe
Asusuna idonka ya na a buɗe
Gama na san yawanci za su ruɗe
Fa Mark ya ba da damar garƙalewa
Fa Ahmadu ya zamo zaɓi na Allah
A tun Ranar ALASTU da anka shela
Ya amsa kan BALE Manzo Rasula
Gaban kowa Ilahu ya ba shi baiwa
Muƙamin nan azal ne ba bu sauyi
Wajen bautar ka ko naci ka ke yi
Ba za ka matso matakin shi Taqiyyi
Muhammadu ya wuce har yai ƙulewa
Idan ranar qiyama anka tashi
Anan ne za ku ƙara sanin irin shi
Wajen ceton da Allah za ya ba shi
Haƙiƙa shi ya zam rahma ga kowa
Da shi ne za'a sa mudun hisabi
Abinda mu kai yaƙini nan da gaibi
A ware ƴan Na'imu da ƴan azabi
Waɗancan na ta kuka mu ko shewa
Da alƙawarin da Allah yai wa Manzo
Na cewa za ya ba shi haɗi da bozo
A ranan nan da ke dako da ta tazo
Idan Allah ya ce bai warwarewa
Fa zai ceto ga duk mai bin sa tabbas
Ma'aiki ne isasshe ɗa ga Abbas
Ta'ala shi ya tsara shi ya zaɓas
A bar yin ja da cewa ya fi kowa
Muhammadu ya fi kowa ya fi kowa
Fa zan ta fada da gunji ba tsayawa
A ko yaushe ku ji ni Muhammadawa
Batun nan ko ba zai daɗi ga kowa
Comments
Post a Comment