SARKIN SARAKUNAN TAUSHI (Hassan Ɗan Thabit)
Roƙon da nayyi ka ban ilmi na domin Ka
Sannan ka ba ni fasaha yanda zan taka
Rawar da ba muguwa ba wajen yabon na Ka
Da shi da dukka sahabban Sidi mai Makka
Allah Gwani na Muhamman inji kakata
Ƙaro dami na salati kan Uban Binta
Alai sahabbai da ƴaƴa har da mai bauta
Bautar Ta'ala da yai Gano da Ɗanbatta
Har masu bin su da kyawu ba su yin shirka
Bayan hakan zan bayanin Mai kiɗan taushi
Hassanu mai kare Manzon nan Maje Arshi
In an taɓa shi ya zam zaryar da ba fashi
Zai kai mari har da gwauro don ya wanke shi
Hassanu Kam ya rabauce babu ko shakka
Kafin zuwan Islama ya zamo gwarzo
Harshensa kansakali mai fauce duk zozo
Zai sulluɓe su da baitoci ya duddurzo
Jinga ake yi da shi gayya idan sun zo
Domin ya kare ƙaɓilu tun ana shirka
Ana cikin haka sai Manzo ya zo da kira
A daina bautar gumaka don a san tsira
Arna su kai dandazo har ma su na kyara
Ga Shugaba na halittun nan Uban Zahra
Hassanu shi ma a loton na cikin harka
Sun tattago shi ya je wai don ya yo nazari
Domin ya san yanda zai zambo ga Albashari
Yayinda yagga Rasulullahi yai marari
Jazba ta kama mawakin har ya na ta ɓari
Baitin yabo ga Rasulullahi Mai Makka
Nan ne ya saƙa kasidar nan ta tasshara
Wannan da ke yi cikin shauƙin cikin halara
Kyawun Ma'aiki ya ce dunyar ga bai tsara
Ya ce Ma'aikin kamar shi yai wa kan sa dira
Sannan yace ba uwar da ta haifi tamkar ka
Da ga nan ya bayyana Imani ya daina sake
In za su je su gumurzu sai ya dau silke
Ya ce ku bar kansakal domin da baki na ke
Hassanu ke ta shiga tsakiya ya na ta cake
Ya na kirari ga Manzo har sahabu duka
Wataran ya ce da Ma'aikin so na ke na zamo
Mai baka duk kariya har ma na kai komo
Kan dukkanin masu cutarwa da sun zarmo
In sun yi zambo ya zamto ni nake ramo
Abinda duk su ka ce kan Sidi mai Makka
Ya ce da shi je ga Siddiq ko na ce Garba
Domin ko shi a Ƙuraishin kwai sanin nasaba
Domin gudun kar wajen sukar su ƴan gaba
Ka je ka sanya da ni Abba ga Zainaba
Don kakanin mu guda ne su su kai shirka
Hassanu nan ya faɗa zan fidda kai Mahi
Tamkar fita da zaren gashi cikin mayhi
Nan ne Ma'aiki ya roƙa mas haɗin Ruhi
Jibrilu mai ƙarfafa da nufi na Lillahi
Ya san rabauta dalilin kare mai Makka
Duk masu bege yabo ga sarakunan dunya
Ba wanda yayyi gamo na katar matso ku jiya
Tamkar su Hassanu sarki mai kiɗan shiriya
Ranar ƙiyama ina son za ni mai rakiya
Girman abinda ka bega shi ya nashe ka
Allah ya ba mu ya taku ba mu kaiwa ku
Na so na zamto ina bin inda kai taku
Fannin yabon Mujtaba ku kun zamo teku
Wa za ya kalle mu in an ce a yau ga ku
Hassanu ƙaunar ka ni zan yi ta ba shakka
Yarda ta Allah a kullum za ta ƙaru ga shi
Domin Ma'aiki na Allah ya kwa yarda da shi
Allahu sanya mu tashi gaban Maje Arshi
Ya dinga zabga yabon mu ko mu na amshi
Allahu amsa du'ain don sa mai Makka
Tsira aminci na Allah kan sa Manzon mu
Ƴaƴa, sahabbai da mataiku iyayen mu
Har masu bin su da kyau hanyar su sun kamu
Ga malamai ƴan uwa ka haɗa iyayen mu
Ya zamo a ranar ƙiyama mun wuce duka
Comments
Post a Comment