TAMBAYAR WALAKIRI

TAMBAYAR WALAKIRI

Bismillah Allah Auwalun kuma Akhiri

Shi Baɗini ne shi ya zam kuma Zahiri


Tsira aminci kan Masoyi Shugaba

Kuma jagabana Mai son mu san alheri


Kan tambayar ƙabari na ke son nai batu

Bar duk abinda ka ke ka ɗan saurari


A Qawa'idi ƙarshen sa za ka duk batun

Ga tambayoyin ga jawabin jeri


Bawa idan ya mace fa tabbas za su zo

A mala'kun da mu ke kira Walakiri


Domin a san matsayin Habibi Mustapha

Matsayinsa na kan tambayar Walakiri


Bayan rufe ka maƙabira kam za su zo

Su su biyun nan Munkarun da Nakiri


Nan za su tashi mutum cikin ƙabari nasa

Sui tambayoyin nan bisa kan tsari


Man Rabbuka? Ma dinuka? Sannan su ce

Me kaƙƙudurce kan Bashiru Naziri?


In har a nan dunya ka na a cikin waɗan-

-da su ke ganin girmansa amsar sauri


Sai Munkarun har ɗan uwansa su ce da shi

Kwanta masoyin Mustapha da sururi


Inko ya zamto masu son fifita son

Wani Gansami kayin sa zai sha mari

 

Wai sai ya ce shi ya ji ne a cikin gari

Zai kasa amsawa a kayin tsari


Nan za ya sha mazga da ƙaton sungumi

Sannan su buɗe mas gidan sa na nari


Dukan su ga guduma, gizago, tsitaka,

Gora da duk kayan uƙabar tsauri


Su kam mala'ikku su na bin Jalla ne

Ba saɓa umarni su na cika amri


Allah ina rokon ka in har za su zo

Amsar na zam bashe su har da sururi


Na san Muhammadu na ka dai bawan ka ne

Kuma shugaban duk mursalai Mukhtari


Kuma ya isar da dukan abinda ya zo da shi

Daidai-wa-daida ba daɗi ba ƙari


Allah dubun tsira daɗo kan Mujtaba

Ƴaƴansa, mataiku, sahabbai ɗori

Comments

Popular posts from this blog

BARAM-BARAM

MAWADDAH

Raina Fansar Ka