WA YAI KAMA TASA DUK BAYI NA RAHMANU?
Bismillah Sarki Gwani Rahimu Rahmanu
Ka ba ni himma cikin bege na Ma'munu
Tsira hada da aminci kan sa Miftahu
Haɗa da albarkatu jinkai na Hannanu
Saka ciki alihi har duk sahabbansa
Da ma su bin su da kyawu duk cikin kaunu
Na ɗauki allo na latarki Ina da nufin
Tsaro yabo a wajen suriki na Usmanu
Na firgice ni a ƙaunar nan ta Manzon mu
Wasu lokutan ma Ina jin na fi majnunu
Riba ta begen Rasulullahi ba ta Sa'a
Duba ga ƙissa ta Ka'abun nan da Hassanu
Yayin da Manzo ya sa neman ruwan jallo
Gun Ka'bu bi ni gaba zan ba ka duk kanu
Zambon da yai wa Ma'aikin ne ya sanya Hakan
An sa a Nemo shi ko da har cikin bunu
Sai ɗan uwansa ya je ya sanar da shi halin
Da ake ciki a gari halin da yai munu
Amma ya ce masa shi Manzon maji ƙai ne
Ga yafiya a wajen Bawan na Rahmanu
A cikin duhu na dare kafin kiran fajaru
Ya je ya kai shi gaban Manzo ya gurfanu
Nan ne ya buɗe kasidar nan da tasshara
BANISSU'ADU da ke bege ga Ma'munu
Daɗin yabon nan ya sanya Ɗaha yayyafe
Har ma ya ba shi tukuici Shugaban Kaunu
Kwai inda ma a yabon Manzo ya mai darasu
Kan babu wai shi takobi ne na Dayyanu
Nan Kun ga inda yabon Manzo ya cece shi
Bayan da anka halsata jinin na Ɗan Qainu
Yabon sa ya zam silar tsira wajen Ka'abu
Haka nan idan kun tuno ƙissa ta Hassanu
Begen ka shi na rike nima Ina da nufin
Samun kusanci da kai ran auna mizanu
Ni ba sani a wajena ba yawan zikri
Amma ina son ka ƙauna babu tammanu
Begen ka shi na rika matsayin wuƙar ƙugu
Domin na samu shiga ƙofa ta Rayyanu
Ni ban yawan azumi kuma ba yawan sallah
Begen ka zai sa na san tarba ta Rilwanu
Manzo Muhammadu dunya ban da tamkar ku
Ahalin ka sanya da ni tamkar ta Salmanu
Rokan na san hikima tamkar ta Hassanu
Wajen yabon ka na san matsayi na sultanu
Shi ne ya san karfafawar Ruhu ba shakka
Tamkar ta Isa na Maryam don yabon na ka
Ni.ma a zam ƙarfafa ta nai ta begen ka
Ba gargada ko guluwwi don su Adnanu
Farfajiya ta ƙiyama sa a nemo ni
Domin na buɗe yabon suriki na Usmanu
Zambar dubu ta salati Jalla mai Iko
Dado su kan Mahmud jika ga Adnanu
Allah da duk malakutu su na salatinsa
Kui sallama da salat in kun yi imanu
Comments
Post a Comment